Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa sashin shari’a na fuskantar kalubale mai yawa da ke bukatar magancewa, hanya guda cikin hanyoyin shi ne shawo kan wadannan matsalolin ta hanyar yi wa kai kyakkyawan nazari tare da gina ingantacciyar mafita.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya bude taron kara wa juna sani ga alkalai, Khadi-khadi, alkalan majistiri da jami’an gudanarwa da sauran ma’aikatan hukumar shari’a ta Jihar Kano, wanda ya gudanar a wurin shakatawa da ke Karamar Hukumar Minjibir a Jihar Kano.
Gwamnan wanda mataimakinsa, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya wakiltar ya ce ya lura da cewa sashin shari’a bangare ne mai zaman kanta wadda alhakin kare hakkin ‘yan kasa tare da samar da dokokin kasa.
Ya kara da cewa shirya wannan taron kara wa juna sanin da ma’aikatar shari’ar ba kawai tunkarar ciyar da tsarin gaba ne kawai ba, har ma da nuna nagartaccen tsari domin sake fasalin ayyukanta na cikin gida ta hanyar samar da wata matsaya da za ta bayar da damar gudanar da kyakkyawan tunani tare da musayar ra’ayoyi kan muhimman batutuwan da ke da alaka da harkokin gudanarwar hukumar shari’a a Jihar Kano.
“Dokar asusun hukumar shari’a ta shekarar 2022 tana da muhimmancin gaske a harkokin mulkin kasancewar ta samar da harsashin nasarar cin gashin kai tare da harkokin kudin ma’aikatar shari’a a Kano,” in ji Ganduje.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp