Kasar Sin tana bin hanyarta mafi dacewa da ita wajen raya harkokin kudi, wadda ta bambanta da irin wacce kasashen yammacin duniya ke bi. Kuma Mr. Xi Jinping ya fara kokarin lalubo hanyar tun shekaru 40 da suka gabata, inda ya yi gyare-gyare ga harkokin kudi, tare da amfani da rancen kudi don sauya daji zuwa “baitulmali”, da taimaka wa masunta yaki da talauci. A ra’ayin shugaba Xi, babban makasudin gudanar da harkokin kudi, shi ne amfanar da daukacin al’umma. Wannan babban ginshiki ne na harkokin kudi masu salon musamman irin na kasar Sin.
ADVERTISEMENT














