• English
  • Business News
Sunday, August 31, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hanyar Da Matasa Za Su Bi Don Ceto Dimokuraɗiyyar Nijeriya Daga Rugujewa

by Alhaji Adamu Rabiu
4 weeks ago
in Labarai
0
Hanyar Da Matasa Za Su Bi Don Ceto Dimokuraɗiyyar Nijeriya Daga Rugujewa
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Lokacin da matasan Najeriya za su hallara a zauren babban taron matasa na ƙasa, daga 7 zuwa 21 ga Yulin 2025 a birnin Abuja, tambaya guda daya ce za ta mamaye tattaunawar a ƙarƙashin jigo mai taken “Gudanar da Mulki da Shiga Harkokin Siyasa”. 

Ta yaya za mu ɗora siyasarmu a kan turba madaidaiciya, sannan kuma mu ceto dimokuraɗiyya daga hannun azzalumai a Nijeriya? A matsayina na mai gabatar da wannan ƙasidar tsarin manufofi zuwa kwamitin shirya taron, ban tsaya kan bayyana matsaloli kadai ba, na zo da cikakken shiri na ceto dimokuraɗiyyar wannan ƙasa. 

Nijeriya na fama da mummunar matsalar rashin kyakkyawan fasilin siyasa, inda masu kuɗin haram ke karɓe jam’iyyun siyasa, fagen siyasa ya zama cike da haɗura da dungu, zaɓe ya koma yaudara, inda wanda ya ci zaɓe shi kadai ke cin moriyarta, ƴan gudun hijira sun rasa damar kada ƙuri’arsu, sannan hukumomin zaɓe na jihohi, sun zama karen farautar masu riƙe da madafun iko a jihohi, sannan suna yi wa gaskiya da riƙon amana riƙon sakainar-kashi. 

  • Yadda Rayuwa Take A Sansanin ‘Yan Gudun Hijira A Nijeriya
  • Hanyar Da Matasa Za Su Bi Don Ceto Demokuradiyyar Nijeriya Daga Rugujewa

Wadannan matsaloli da wasu ma, na buƙatar matasa su yi karatun ta-nutsu, su kuma  dauki matakin gaggawa; domin ceto Nijeriya daga hannun azzalumai, kana su kuma ɗora ta a kan turba madaidaiciya. 

Matsalolin da Muke Fuskanta:                    

Labarai Masu Nasaba

Ko Zuwan Rasha Afirka Zai Inganta Tsaro A Yankin Sahel?

Babban Taron Lauyoyi Na Kasa: Sarkin Musulmi Ya Gargadi Alkalai Kan Tabbatar Da Adalci

Bayan shekar 22 da kuɓutar da Nijeriya daga mulkin soja, dimokuraɗiyya na ci gaba da fama da rauni mai tsanani. Alamun cutar sun bayyana ne a cinikin baragurbin wakilai (delegates), amfani da kuɗin ƙasa da aka wawure ta hanyar haram wajen gudanar da yaƙin neman zaɓe, maƙudan kuɗin da ake ware wa Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC), ƙarancin yawan masu kada ƙuri’a, sayen ƙuri’u a bainar jama’a, tashin hankali yayin zaɓe, da kuma yaɗuwar fargaba, musamman a tsakanin matasa, cin amana na ƴan siyasa, canja sheƙa da zaɓaɓɓu ke yi, da dai sauran makamantansu.                                       

Asalin matsalar ita ce, rashin shiga cikin gudanar da gwamnati a siyasance (eɗclusion) na masu gaskiya da riƙon amana, matasa, mata, masu fama da naƙasa, ƴan gudun hijira da jam’iyyun da ke da ƙaramin ƙarfi, duk sun kasance a wajen filin. 

Wannan ba kawai rashin adalci ba ne, har ma ya saɓa wa kundin tsarin mulki, kuma barazana ce ga zaman lafiya da ci gaban ƙasa. Idan ka duba, za ka fahimci cewa; dimokuraɗiyyarmu na hannun wasu tsirarun mutane da shugabannin jam’iyyu masu ƙarfi, wadanda suka killace matasa da sauran ƴan Nijeriya daga samun damar shiga siyasa ko a saurare su ko la’akari da tasu gudunmawar. ɗimokuraɗiyyar cikin gida a jam’iyyu, abin dariya ne kawai, domin an mayar da zaɓe na cikin gida zuwa ciniki, wato ba ni kuɗi ga ƙuri’a. Inda a wani ɓangaren kuma, INEC na fuskantar ƙalubalen rashin ƴanci da rashin ƙwarin guiwar aiwatar da dokokinta. 

Har ila yau, ƴan gudun hijira da sauran al’umma masu rinjaye ana ci gaba da ware su daga zaɓe. Haka nan, hukumar zaɓen jihohi, musamman yadda aka gani a zaɓen ƙananan hukumomi a Kaduna da Bauchi, sun zama wani kwafi da ya ci mutuncin dimokuraɗiyya. Wannan ya saɓa wa sassa da dama na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (Sashe 14(2)(a), 15(1), 40, 153(1)(f), 221, 318(1), da Jadawali na Bakwai), da ɗokokin ƙungiyar Tarayyar Afirka da kuma Majalisar ɗinkin ɗuniya.   

Yadda Wannan Tsari Na Matasa Zai Taimaka Wajen Ceto Siyasarmu:

1-Yarjejeniya Ta ƙasa ɗon Siyasa Mai Inganci (National Charter for Inclusion): A samar da wata Yarjejeniya ta haɗin gwiwa tsakanin Ma’aikatar Matasa ta ƙasa, ƙungiyar Gamayyan Jamíyyun Siyasa (IPAC), Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC), ƙungiyoyin Fararen Hula da Majalisar Matasa ta Nijeriya. Wannan yarjejeniya za ta kafa ƙa’idoji da dokokin da za su tilasta dimokuraɗiyya a cikin jam’iyyu, tabbatar da adalci wajen zaɓuɓɓuka da kuma bai wa dukkannin jam’iyyun da suka shiga zaɓe damar ba da gudunmuwa wajen shugabanci a kowane mataki da kuma bai wa matasa, mata, ƴan gudun hijira da kowa da kowa damar ƴancin tsayawa takara cikin adalci.  

2- Sauyi Mai Zurfi Ga Jam’iyyu da Tsarin Zaɓe:

Ya zama wajibi jam’iyyu su buɗe ƙofa. A kafa dokar da za ta tilasta duk mai son tsayawa takara gabatar da “Tsarin Ayyuka” (Project Plans) kafin hawa kujera, sannan ya fitar da “Rahoton ƙarshe” (End-of-Term Reports), bayan barin gado ko da kuwa zai koma kuwa. A daƙile kuɗin da ake nema marasa tushe daga masu neman takara, musamman na hukumomin zaɓen jihohi, (Misalin KAɗ-SIECOM). A tabbatar da cikakken amfani da Sashe na 7 na Kundin Tsarin Mulki da ɗokar Zaɓe ta 2022.   

3- Runguman ɗimokuraɗiyyar ɗijital Hannu Biyu (ɗigital ɗemocracy): 

A kafa “Cibiyar ɗimokuraɗiyyar ɗijital ta ƙasa (NɗɗH)” da za ta sa ido, bayar da rahoto kai tsaye, sa ido kan kuɗin yaƙin neman zaɓe da tantance tsarin jam’iyyu. Za ta kuma ba da damar samun ilimin siyasa ta hanyar wasanni da fasahar zamani domin ƙara fahimta, rage rashin sha’awa daga matasa, da bunƙasa ilimi da riƙon amana. 

4- Ƙarfafa IPAC Youth da Shirye-shiryen Fadakarwa: 

A ƙarfafa ɓangaren Matasa na IPAC (IPAC Youth ɗirectorate) daga matakin ƙasa har zuwa jihohi, ta hanyar samar da doka, kasafin kuɗi da kuma tsarin aiki. Sannan, a ɗora musu alhakin wayar da kan jama’a a faɗin ƙasar nan, musamman a tsakanin wadanda aka ware daga siyasa. 

Me Za Mu Samu Idan An Bi Wannan Hanya? Za mu samu dimokuraɗiyya mai inganci da kuma tsabta, inda matasa, mata, masu fama da nakasa (PWɗs) da ƴan gudun hijira (IɗPs) za su samu bakin fada kuma a ji a cikin siyasa da shugabanci. Za a samu ƙarancin tashin hankali a lokacin zaɓe, raguwar sayen ƙuri’a da ingantaccen ilimi da wayewa a tsakanin jama’a.  Za kuma a samu jam’iyyu masu gaskiya da amana da kuma shugabanci na ƙwarai da ci gaban ƙasarmu Nijeriya. 

Matakan Aiwanar da Wannan Tsari: 

Mataki na 1:

Rubuta NSPPC tare da dukkan masu ruwa da tsaki.

Mataki na 2: Kafa tsarin dubawa tsakanin INEC, IPAC da CSO.

Mataki na 3: ƙaddamar da NɗɗH da kayan aikin ilmantarwa.

Mataki na 4: Gyaran ɗokar Zaɓe, domin shigar da wadanan al‘amura da muka gabatar a sama da sauran buƙatu. 

Kafin Mu Kammala: Makomar dimokuraɗiyyar Nijeriya na cikin hadari. Ba za mu iya ci gaba da kallon halin da ake ciki ba na rashin adalci, cin amana, zangon ƙasa ga ƙasa da al’úmarta. 

Yazama wajibi mu yi amfani da ƙarfin matasa, domin ceto Nijeriya daga bakin kuraye. ƙirƙire-ƙirƙire da buƙatar riƙon amana, su ne maganin cutar da dimokuraɗiyyarmu ke fama da ita. 

Wannan tsari nawa na zuwa ne daga gwanancewa da aiki da IPAC, shirye-shiyen fitar da saƙwanni ta ‘Bakondare Speaks’, wallafa rubuce-rubuce a manyan jaridu kamar su Premium Times, daily Trust, Guardian, Punch, Vanguard, Thisday , Leadership (A hausance da turanci)) da kuma shiga ayyukan siyasa masu tsafta da kuma alaƙa da ƙungiyoyi masu muhimmanci na siyasa.   

Yanzu ne lokacin sauyi! Muryar matasa ya kamata ta koma tsakiya wajen tsara manufofi da aiwatar da su. Yakamata dimokuraɗiyyar Nijeriya ta amfani kowa da kowa ba wasu ba kawai! 

Kafin rahoton ƙarshe na wannan taro ya isa ofishin Shugaban ƙasa ranar 12 ga Agusta, 2025 (Ranar Matasa ta ɗuniya), ina kira da babbar murya da fatan alheri ga duk dan Nijeriya da kuma dukkan wakilai da su rungumi wannan tsari. Ina kuma kira ga ƴan majalisa da masu zartarwa da su aiwatar da shi, domin ci gaban Nijeriya da kuma amfanin masu zuwa nan gaba. Yanzu ne lokacin daukar mataki na haƙiƙa da Jarumta! Allah ya yi mana albarka, ameen.

 


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Sin Ta Samu Bunkasar Tafiye-Tafiye Cikin Gida Da Kashi 20.6% A Rabin Farko Na Bana

Next Post

Sin Ta Kadu Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Wa Hukumomi Da Jami’an Falasdinu

Related

Ko Zuwan Rasha Afirka Zai Inganta Tsaro A Yankin Sahel?
Labarai

Ko Zuwan Rasha Afirka Zai Inganta Tsaro A Yankin Sahel?

48 minutes ago
Gidauniyar ‘Ya’yan Sarakunan Arewa Sun Marawa Sarkin Musulmi A Matsayin Shugaban Majalisar Sarakuna
Rahotonni

Babban Taron Lauyoyi Na Kasa: Sarkin Musulmi Ya Gargadi Alkalai Kan Tabbatar Da Adalci

21 hours ago
Sin Ta Fara Amfani Da Tauraron Dan Adam Wajen Duba Manyan Hanyoyin Wutar Lantarki A Karo Na Farko
Rahotonni

Cire Tallafin Wutar Lantarki Zai Kara Kuntata Rayuwar ‘Yan Nijeriya – Kungiyar Kwadago

22 hours ago
Legas Ta Laƙume Aikin Naira Tiriliyan 3.9 Cikin Shekaru Biyun Tinubu
Manyan Labarai

Legas Ta Laƙume Aikin Naira Tiriliyan 3.9 Cikin Shekaru Biyun Tinubu

22 hours ago
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas
Tsaro

‘Yansanda Sun Ceto Wani Dan Shekara 25 Da Aka Sace A Jihar Kebbi

1 day ago
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi
Tsaro

An Cafke Mutum Hudu Bayan ‘Yan Fashi 20 Sun Afka Wasu Gidaje A Bauchi

1 day ago
Next Post
Sin Ta Kadu Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Wa Hukumomi Da Jami’an Falasdinu

Sin Ta Kadu Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Wa Hukumomi Da Jami’an Falasdinu

LABARAI MASU NASABA

Ko Zuwan Rasha Afirka Zai Inganta Tsaro A Yankin Sahel?

Ko Zuwan Rasha Afirka Zai Inganta Tsaro A Yankin Sahel?

August 31, 2025
Yadda Kungiyoyin Firimiyar Ingila Suka Shirya Wa Kakar Bana

Yadda Kungiyoyin Firimiyar Ingila Suka Shirya Wa Kakar Bana

August 31, 2025
‘Yan Wasan Afirka Da Ake Ganin Za Su Yi Abin Kirki A Kakar Bana

‘Yan Wasan Afirka Da Ake Ganin Za Su Yi Abin Kirki A Kakar Bana

August 31, 2025
tusar gaba

Ko Kin San… Dalilin Da Ke Sa Mata Ke Ganin Farin Ruwa Kafin Ko Bayan Al’adarsu?

August 31, 2025
Masana’antar Kannywood Na Tsananin Buqatar Addu’a – Hauwa Garba

Masana’antar Kannywood Na Tsananin Buqatar Addu’a – Hauwa Garba

August 31, 2025
Me Ya Sa Wasu Maza Ke Gudun Auren Mata ‘Yan Boko Masu Kwarewa Da Wayewa?

Me Ya Sa Wasu Maza Ke Gudun Auren Mata ‘Yan Boko Masu Kwarewa Da Wayewa?

August 31, 2025
Shugaban Kasar Sin Ya Gana Da Firaministan Kasar Masar

Shugaban Kasar Sin Ya Gana Da Firaministan Kasar Masar

August 30, 2025
Ranar Hausa: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka

Ranar Hausa: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka

August 30, 2025
Xi: Har Kullum Sin Za Ta Kasance Amintacciyar Abokiyar Huldar MDD

Xi: Har Kullum Sin Za Ta Kasance Amintacciyar Abokiyar Huldar MDD

August 30, 2025
Gyaran fuska

Gyaran Fuska Da Laushin Fata

August 30, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.