Corset, wani tufafi ne da ake sawa don gyara suffa ko matse kugu da goyan bayan kirji, wadda ya kasance a matsayin tufafi tun daga tushe na zamanin kayan ado na waje.
A lokacin farkon zamanin corsetry, abin ado da ake kira da corsets ya fara ne kafin karni na 19 wanda yake tare da gyara kasusuwan mace -ya gyaggyara saman jikin mace zuwa suffar B kuma ya baje tare da tura kirjin.
- Gwamnan Gombe Ya Gabatar Da Naira Biliyan 173.697 A Matsayin Kasafin 2023
- Manoman Alkama 200 Za Su Amfana Da Shirin NALDA A Jihar Jigawa
Wasu an hada su da riguna ko za a iya daure su da su domin a adana suffa mai fadi a kugu. Daga baya, da kwalliya ta kara wanzuwa an canza shi zuwa zuwa abin ado mafi kyau ga mata.
Haka zalika a wannan zamanin corset ya kasance abu mafi muhimmanci da mata suke Amfani da shi wajen kawata kwalliyansu musamman a lokacin bukukuwa.
A wannan Mukala tamu ta yau na kawo muku hanyoyin da za ku bi wajen amfani da kwalliyan corset musamman ga amare.
Na farko da kuma mafi mahimmancin shi ne ki nemo corset wanda ya dace da nau’in jikinki, wanda kuma zai dace da shi daidai. Wasu su kan yi amfani da shi a bayyane, wasu kuma ana yi musu amfani da shi a sirrance wadda shi ne abu mafi kyau musamman a al’adanmu na Arewa. Haka zalika akwai na’uka na corset wadda sai kin kula sosai kafin ki cire mai kyau.
Abu na biyu shi ne idan kika samu nasarar samun corset mai dacewa, to, zai iya ba da cikakken goyon baya ga jikinki, wanda zai taimake ki kula da daidaitattuwarki. Haka nan corset zai taimaka miki wajen inganta yanayin tsarin jikinki. Saboda wadannan dalilai, samun corset mai dacewa yana da mahimmanci. Don haka, ki tabbatar da sanin suffar jikinki kuma ki tuntubi masana don sanin nau’in corset wanda zai iya taimakawa masu lankwasa daidai.
Daga karshe kuma ki tabbatar da cewa kayan da za ki yi dinkin a jiki kayane na biki ba wain a zaman gida ba, domin kuwa kwalliyar corset ta fi dacewa da kayan zuwa wani taro.
Daga shafin UMMU KHULTHUM ABDULKADIR.