Gwagwarmayar da Nijeriya ke yi domin kawo karshen ayyukan ta’addanci da karuwar ‘yan ta’adda ya kai kololuwar matak. Abin takaicin shi ne yadda kasar nan ke ci gaba da fuskantar komabaya da matsaloli sakamakon ayyukan ta’addanci ta yadda aka dora Nijeriya a matsayin kasa ta takwas da harkokin ta’addanci ya yi wa gaggarumin illa a duniya, kamar yadda kungiyar nan mai suna “Global Terrorism Inded” ta bayar da rahoto a shekarar 2023.
Abubuwan da ke haifar da yaduwar akidun ta’addanci sun hada da wa’azozin miyagun malaman addini, masu habbaka ra’ayoyin kabilanci da wasu mugayen kungiyoyi masu hatsari ga rayuwar al’umma, haka kuma kawar da kai daga hakokokin al’umma da mahukunta ke yi yana haifar da tashin tashina a zukatan matasa wanda hakan yake haifar da rashin kwanciyar hankali a siyasance.
- EFCC Za Ta Fara Amfani Da Fasahar Zamani Wajen Gano Masu Ɗaukar Nauyin Ta’addanci
- Ƴan Ta’addan Da Suka Kai Hari Borno Zasu Yabawa Aya Zaƙinta – Tinubu
Kamar yadda Hukumar Majalsiar Dinkin duniya mai kula safarar miyagun kwayoyi da manyan laifukka ta bayyana, Nijeriya na fuskantar manyan kalubale daga ayyukan ta’addanci da kuma ayyukan yaki da ta’addancin da hukumomi ke yi, musamman in muka lura da harkokin ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso gabas da sauran bangarorin Nijeriya. Sakamakon wadannan kuma shi ne mace-macen fararen hula, tarwatsa al’umma daga muhallansu da kuma asara ga tattalin arzikin al’umma wanda ke haifar da karin talauci a tsakaninsu.
A bayyana yake cewa, ta’addanci na samun gindin zama ne in aka samu wasu kafofi da suka hada da rauni daga gwamnati mai ci, rashin adalci daga gwamnati ga al’umma, iyakokin kasa da basu da inganci, talauci, rashin aikin yi da jahilici a tsakanin mutanen kasa, da sauran sakaci da ke faruwa daga gwamnatin a kan al’umma.
Wani bincike da wata kungiya mai suna (CISLAC) ta yi wanda hukumar GIABA-ECOWAS ta dauki nauyi ya nuna cewa, rashin fadakar da al’uamma a yankun karkara na bukatar su bayar da bayanan sirri ga jami’an tsaro a lokacin da ya dace ya kara ta’azzara ayyukan ‘yan ta’addan a yankin arewa maso gabas, kamar yadda aka samu wasu kungiyoyin sa kai da suke tallafa wa gwamnati a yakin da ake yi da ta’addanci.
Yana da matukar muhimmanci a fahimci cewa, rashin cikakken fadakar da al’umma a kan hakkin da ya doru a kan su na bayar da bayanan sirri ga jami’an tsaro a yakin da ake yi da ta’addanci yana taimakwa wajen rashin nasarar da ake yi a yaki da ta’addanci a matakai daban-daban.
Bayani ya nuna cewa, rashin ingantattantun iyakokin kasa yana sa ‘yan ta’adda na amfani da shi wajen shiga da fitar da kayayayykin su na ayyukan ta’addanci ba tare da hukuma ta iya sanya ido ba. Nijeriya nada iyaka da kasa Nijar ta arewacin kasa, a arewa maso gabas kuma ta yi iyaka da kasar Chadi a gabas kuma ta yi iyaka da Kamaru, a yammacin kasa kuma ta yi iyaka da kasa Benin, a kiddigar da aka yi a shekarar 2016, Nijeriya nada iyakoki fiye da 1,500 amma a cikin wadannan 114 ne kawai jami’an tsaro ke iya sa ido a kai amma sauran babu wani jami’i da ke lura da abin da ake shiga da fita wannan yana taimakawa wajen ayyukan ta’addancin da ake fuskanta a sassan NIjeriya.
Ba zai yiwu mu manta da rawar da talauci da harkokin tattalin arziki ke takawa wajen zafafa ayyukan ta’addanci da ‘yan ta’adda ba, hakan yana taimaka musu wajen samun saukin daukar sabbin ‘yan ta’adda ta hanyar amfani da kudade dan kadan suna yaudarar matasa. Abubuwan da suka faru a arewa maso gabas inda wasu ‘yan kalilan a cikin al’umma suka rungumi akidar ta’addanci sakamakon yadda aka yi watsi da su a harkokin tafiyar da gwamnati ya ishe mu misali.
Haka kuma a wani rahoto na USAID da aka fitar a shekarar 2017 ya nuna cewa, bai kamata a mayar da hankali kacokan a kan yaki da ta’addanci ba tare da ana kuma samar da ababen more rayuwa da za su taikama wajen rage radadin talauci da tsadar rayuwa da al’umma ke fuskanta ba domin sune suke saurin taimaka wa ‘yan ta’adda yada mugayen ra’ayoyinsu a cikin al’umma.
Wani abu mai matukar muhimmanci kuma shi ne ganin yadda ‘yan ta’adda ake bukatar ababen tafiyar da rayuwa kamar kudade domin sayen makamai da daukar sabbin abokan aiki, sai gashi bangaren cibiyoyin kudi musamman bankuna suna basu damar mu’amala da kudade ba tare da wata matsala ba duk kuwa da an san kudaden haramun ne.
Bincike ya nuna yadda ‘yan ta’adda ke amfani da bankuna wajen karbar kudaden fansa daga al’umma suna kuma safarar miyagun kwayoyi da cinikin makamai ta bankuna amma bankuna sun kasa taka musu birki.
A kan haka ya zama dole a dauki matakan da suka kamata da sanya ido a kan zirga-zirgar kudade ta hanyar sanya sabbin dokoki da bankuna za su yi amfani da su wajen dakile masu safarar, musamman masu canji da ‘yan POS da sauran hanyoyin aikawa da karbar kudi a kasar nan, domin ta nan ne masu daukar nauyin ta’addanci ke amfani wajen aikata muggan ayyukansu.
Yana kuma da matukar muhimmanci a yi gangammin yaki da talauci a tsakanin al’umma da kuma yaki da jahilci, a yi amfani da malaman addini wajen ganin wasu taba gari basu shigo da rigar addini suna bata fikirar al’umma ba. A kan haka ya kamata a samar da dokokin da zai sa ido a kan yadda malamai ke gudanar da wa’azozinsu.
Ta wadanna hanyoyi, ana fatan Nijeriya ta samu nasarar dakile muggan ra’ayoyi na ‘yan ta’adda da yadda yake yaduwa a cikin al’umma ta yadda za mu samu tsayayyar kasa da ta tsira daga tashin hankalin ta’addanci da na ‘yan ta’adda.