ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, July 5, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hanyoyin Dakile Ta’addanci Da ‘Yan Ta’adda

by Ra'ayinmu
2 years ago
Hanyoyin Dakile

Gwagwarmayar da Nijeriya ke yi domin kawo karshen ayyukan ta’addanci da karuwar ‘yan ta’adda ya kai kololuwar matak. Abin takaicin shi ne yadda kasar nan ke ci gaba da fuskantar komabaya da matsaloli sakamakon ayyukan ta’addanci ta yadda aka dora Nijeriya a matsayin kasa ta takwas da harkokin ta’addanci ya yi wa gaggarumin illa a duniya, kamar yadda kungiyar nan mai suna “Global Terrorism Inded” ta bayar da rahoto a shekarar 2023.

Abubuwan da ke haifar da yaduwar akidun ta’addanci sun hada da wa’azozin miyagun malaman addini, masu habbaka ra’ayoyin kabilanci da wasu mugayen kungiyoyi masu hatsari ga rayuwar al’umma, haka kuma kawar da kai daga hakokokin al’umma da mahukunta ke yi yana haifar da tashin tashina a zukatan matasa wanda hakan yake haifar da rashin kwanciyar hankali a siyasance.

  • EFCC Za Ta Fara Amfani Da Fasahar Zamani Wajen Gano Masu Ɗaukar Nauyin Ta’addanci 
  • Ƴan Ta’addan Da Suka Kai Hari Borno Zasu Yabawa Aya Zaƙinta – Tinubu

Kamar yadda Hukumar Majalsiar Dinkin duniya mai kula safarar miyagun kwayoyi da manyan laifukka ta bayyana, Nijeriya na fuskantar manyan kalubale daga ayyukan ta’addanci da kuma ayyukan yaki da ta’addancin da hukumomi ke yi, musamman in muka lura da harkokin ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso gabas da sauran bangarorin Nijeriya. Sakamakon wadannan kuma shi ne mace-macen fararen hula, tarwatsa al’umma daga muhallansu da kuma asara ga tattalin arzikin al’umma wanda ke haifar da karin talauci a tsakaninsu.

ADVERTISEMENT

A bayyana yake cewa, ta’addanci na samun gindin zama ne in aka samu wasu kafofi da suka hada da rauni daga gwamnati mai ci, rashin adalci daga gwamnati ga al’umma, iyakokin kasa da basu da inganci, talauci, rashin aikin yi da jahilici a tsakanin mutanen kasa, da sauran sakaci da ke faruwa daga gwamnatin a kan al’umma.

Wani bincike da wata kungiya mai suna (CISLAC) ta yi wanda hukumar GIABA-ECOWAS ta dauki nauyi ya nuna cewa, rashin fadakar da al’uamma a yankun karkara na bukatar su bayar da bayanan sirri ga jami’an tsaro a lokacin da ya dace ya kara ta’azzara ayyukan ‘yan ta’addan a yankin arewa maso gabas, kamar yadda aka samu wasu kungiyoyin sa kai da suke tallafa wa gwamnati a yakin da ake yi da ta’addanci.

LABARAI MASU NASABA

Yajin Aiki: Ƙungiyar Likitocin Nijeriya Ta Ba Gwamnati Wa’adin Mako Huɗu

Rashin Tarbiyya Da Ilimin Addini Ne Ke Sa Matasa Ɗaukar Doka a Hannu – Hon. Aminu Adam

Yana da matukar muhimmanci a fahimci cewa, rashin cikakken fadakar da al’umma a kan hakkin da ya doru a kan su na bayar da bayanan sirri ga jami’an tsaro a yakin da ake yi da ta’addanci yana taimakwa wajen rashin nasarar da ake yi a yaki da ta’addanci a matakai daban-daban.

Bayani ya nuna cewa, rashin ingantattantun iyakokin kasa yana sa ‘yan ta’adda na amfani da shi wajen shiga da fitar da kayayayykin su na ayyukan ta’addanci ba tare da hukuma ta iya sanya ido ba. Nijeriya nada iyaka da kasa Nijar ta arewacin kasa, a arewa maso gabas kuma ta yi iyaka da kasar Chadi a gabas kuma ta yi iyaka da Kamaru, a yammacin kasa kuma ta yi iyaka da kasa Benin, a kiddigar da aka yi a shekarar 2016, Nijeriya nada iyakoki fiye da 1,500 amma a cikin wadannan 114 ne kawai jami’an tsaro ke iya sa ido a kai amma sauran babu wani jami’i da ke lura da abin da ake shiga da fita wannan yana taimakawa wajen ayyukan ta’addancin da ake fuskanta a sassan NIjeriya.

Ba zai yiwu mu manta da rawar da talauci da harkokin tattalin arziki ke takawa wajen zafafa ayyukan ta’addanci da ‘yan ta’adda ba, hakan yana taimaka musu wajen samun saukin daukar sabbin ‘yan ta’adda ta hanyar amfani da kudade dan kadan suna yaudarar matasa. Abubuwan da suka faru a arewa maso gabas inda wasu ‘yan kalilan a cikin al’umma suka rungumi akidar ta’addanci sakamakon yadda aka yi watsi da su a harkokin tafiyar da gwamnati ya ishe mu misali.

Haka kuma a wani rahoto na USAID da aka fitar a shekarar 2017 ya nuna cewa, bai kamata a mayar da hankali kacokan a kan yaki da ta’addanci ba tare da ana kuma samar da ababen more rayuwa da za su taikama wajen rage radadin talauci da tsadar rayuwa da al’umma ke fuskanta ba domin sune suke saurin taimaka wa ‘yan ta’adda yada mugayen ra’ayoyinsu a cikin al’umma.

Wani abu mai matukar muhimmanci kuma shi ne ganin yadda ‘yan ta’adda ake bukatar ababen tafiyar da rayuwa kamar kudade domin sayen makamai da daukar sabbin abokan aiki, sai gashi bangaren cibiyoyin kudi musamman bankuna suna basu damar mu’amala da kudade ba tare da wata matsala ba duk kuwa da an san kudaden haramun ne.

Bincike ya nuna yadda ‘yan ta’adda ke amfani da bankuna wajen karbar kudaden fansa daga al’umma suna kuma safarar miyagun kwayoyi da cinikin makamai ta bankuna amma bankuna sun kasa taka musu birki.

A kan haka ya zama dole a dauki matakan da suka kamata da sanya ido a kan zirga-zirgar kudade ta hanyar sanya sabbin dokoki da bankuna za su yi amfani da su wajen dakile masu safarar, musamman masu canji da ‘yan POS da sauran hanyoyin aikawa da karbar kudi a kasar nan, domin ta nan ne masu daukar nauyin ta’addanci ke amfani wajen aikata muggan ayyukansu.

Yana kuma da matukar muhimmanci a yi gangammin yaki da talauci a tsakanin al’umma da kuma yaki da jahilci, a yi amfani da malaman addini wajen ganin wasu taba gari basu shigo da rigar addini suna bata fikirar al’umma ba. A kan haka ya kamata a samar da dokokin da zai sa ido a kan yadda malamai ke gudanar da wa’azozinsu.

Ta wadanna hanyoyi, ana fatan Nijeriya ta samu nasarar dakile muggan ra’ayoyi na ‘yan ta’adda da yadda yake yaduwa a cikin al’umma ta yadda za mu samu tsayayyar kasa da ta tsira daga tashin hankalin ta’addanci da na ‘yan ta’adda.

Hanyoyin Dakile
Ra'ayinmu
+ postsBio
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Kisan Gillar Marabar Jos: Bai Kamata Jinin Malama Ummulkhairi Ya Tafi A Banza Ba
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Shin Nijeriya Ta Shirya Tunkarar Dawowar Annobar Ebola?
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Buƙatar Samar Da Alƙibla Ta Musamman Ga Gidajen Gyaran Hali Na Ƙasar Nan
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Ce-ce-ku-ce Kan Batun Biyan Bashin Naira Tiriliyan 3.3 Na Kuɗin Lantarki

MASU ALAKA

Matsalar Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Taimakon Ƙasashen Waje
Labarai

Yajin Aiki: Ƙungiyar Likitocin Nijeriya Ta Ba Gwamnati Wa’adin Mako Huɗu

July 5, 2026
Rashin Tarbiyya Da Ilimin Addini Ne Ke Sa Matasa Ɗaukar Doka a Hannu – Hon. Aminu Adam
Labarai

Rashin Tarbiyya Da Ilimin Addini Ne Ke Sa Matasa Ɗaukar Doka a Hannu – Hon. Aminu Adam

July 5, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Allah-Wadai Da Kisan ‘Ƴan Nijeriya 2 A Afrika Ta Kudu
Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Allah-Wadai Da Kisan ‘Ƴan Nijeriya 2 A Afrika Ta Kudu

July 5, 2026
Next Post
Tsarin ‘Yancin Kasuwanci A Afirka: Nijeriya Za Ta Amfana Da Dala Biliyan 50 

Tsarin ‘Yancin Kasuwanci A Afirka: Nijeriya Za Ta Amfana Da Dala Biliyan 50 

LABARAI MASU NASABA

FIFA Ta Dakatar Da Aiwatar Da Hukuncin Hana Folarin Balogun Buga Wasa

FIFA Ta Dakatar Da Aiwatar Da Hukuncin Hana Folarin Balogun Buga Wasa

July 5, 2026
Sabbin Shaidu Sun Bulla Dake Kara Tabbatar Da Ta’asar Amfani Da Sinadarai Masu Guba Yayin Da Dakarun Japan Ke Mamaya A Sassan Kasar Sin

Sabbin Shaidu Sun Bulla Dake Kara Tabbatar Da Ta’asar Amfani Da Sinadarai Masu Guba Yayin Da Dakarun Japan Ke Mamaya A Sassan Kasar Sin

July 5, 2026
Matsalar Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Taimakon Ƙasashen Waje

Yajin Aiki: Ƙungiyar Likitocin Nijeriya Ta Ba Gwamnati Wa’adin Mako Huɗu

July 5, 2026
An Gabatar Da Littafin “Bayanan Xi Jinping Kan Basirar Gudanar Da Ayyuka A Kananan Hukumomi”

An Gabatar Da Littafin “Bayanan Xi Jinping Kan Basirar Gudanar Da Ayyuka A Kananan Hukumomi”

July 5, 2026
Ko Kafa Ƴansandan Jihohi Zai Taimaka Wajen Kawo Ƙarshen Matsalolin Tsaro?

Ko Kafa Ƴansandan Jihohi Zai Taimaka Wajen Kawo Ƙarshen Matsalolin Tsaro?

July 5, 2026
Rashin Tarbiyya Da Ilimin Addini Ne Ke Sa Matasa Ɗaukar Doka a Hannu – Hon. Aminu Adam

Rashin Tarbiyya Da Ilimin Addini Ne Ke Sa Matasa Ɗaukar Doka a Hannu – Hon. Aminu Adam

July 5, 2026
Kayayyakin Sin Sun Jawo Hankalin Sassan Kasa Da Kasa

Kayayyakin Sin Sun Jawo Hankalin Sassan Kasa Da Kasa

July 5, 2026
Sin Da Rasha Za Su Gudanar Da Atisayen Sojojin Ruwa Da Sintiri Na Hadin Gwiwa

Sin Da Rasha Za Su Gudanar Da Atisayen Sojojin Ruwa Da Sintiri Na Hadin Gwiwa

July 5, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Allah-Wadai Da Kisan ‘Ƴan Nijeriya 2 A Afrika Ta Kudu

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Allah-Wadai Da Kisan ‘Ƴan Nijeriya 2 A Afrika Ta Kudu

July 5, 2026
Tawagar Jami’an Lafiya Ta Sin Ta Kafa Cibiyar Horar Da Ma’aikatan Jinya A Saliyo

Tawagar Jami’an Lafiya Ta Sin Ta Kafa Cibiyar Horar Da Ma’aikatan Jinya A Saliyo

July 5, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.