Cutar Basir da ake kira da ‘Hemorrhoids’ ko ‘Piles’ a turance, larura ce da ke ci gaba da shan gurguwar fahimta a tsakanin al’umma.
A likitance, ba wani abu ne Basir ba; face kumburarrun jijiyoyin jini a cikin karshen babban hanji da kuma dubura. Wadannan kumburarrun jijiyoyin jinin, su ne suke talewa har su yi bulli cikin karshen babban hanji ko kewayen dubura.
- Koyo Daga Tarihi Da Kiyaye Zaman Lafiya Za Su Sa Kaimi Ga Zamanantar Da Duk Duniya Baki Daya
- Maulidi: Gwamnan Zamfara Ya Taya Al’ummar Musulmi Murna, Ya Buƙaci A Dage Da Addu’o’in Samun Zaman Lafiya
Har ila yau, Basir a cikin karshen babban hanji shi ne, Basir cikin dubura, yayin da Basir a kewayen dubura kuma shi ne Basir wajen dubura.
Haka nan, Basir mai tsiro; ci gaban Basir cikin dubura ne, wanda ke bayyana yayin da matsalar ta je matakin karshe. Basir mai tsiro, na faruwa ne sakamakon zazzagowa ko saukowar jijiyoyin jinin da suka yi bulli zuwa wajen dubura, musamman yayin yunkuri.
Alamomin Basir
Bayyanar alamomin Basir, ya danganta ga wane irin Basir ne ya bayyana, Basir cikin dubura ko kuma Basir a wajen dubura?
Alamomin Basir Cikin Dubura:
1- Zubar jini ba tare da jin ciwo ba, a yayin tsuguno.
2- Basir mai tsiro, wanda ke fitowa wajen dubura; har sai an tura da yatsa, domin mayar da shi. Yana haifar da ciwo da radadi.
Alamomin Basir A Wajen Dubura:
1- Ciwo mai radadi
2- Kaikayi
3- Kumburi a kewayen dubura
4- Zubar jini yayin yunkurin tsuguno
Abuban da ke kawo Basir: Basir na faruwa ne sakamakon takura jijiyoyin jini a dubura, har su kumbura sannan su yi bulli saboda abubuwa kamar haka:
1- Yawan yunkuri yayin tsuguno
2- Tsawaitar lokacin tsuguno
3- Fama da atini ko kuma taurin bayan gida tsawon lokaci
4- Kasancewa mai kiba ko teba.
5- Kasancewa mai juna biyu
6- Cin abincin mai karancin dusa, harza ko ganyayyaki
7- Daga nauyi akai-akai da sauran makamantansu
Hanyoyin Kiyaye Basir Cikin Sauki
Hanya mafi kyau wajen kiyaye kai daga basir ita ce, sanya bayan gida ya zamo mai taushi yadda zai fice ba tare da yunkuri sosai ba.
Wadannan hanyoyi, za su taimaka wajen kiyaye kai daga Basir da kuma rage matsalolinsa:
1- Cin abinci mai dusa sosai: Abinci mai dusa ya hada da ‘ya’yan itatuwa, ganyayyaki da kuma datsar hatsi.
2- Shan isasshen abin sha: Shan isasshen ruwa akalla lita biyu zuwa uku a kowace rana da sauran ababen sha masu ruwa-ruwa.
3- Rage yunkuri yayin tsuguno: Yunkuri tare da rike numfashi yayin tsuguno na takura jijiyoyin jini a cikin dubura.
4- Garzayawa da zarar jin bayan gida: Yin buris da bayan gida yayin da aka ji shi, na jawo jiki ya ci gaba da tsotse ruwan bayan gidan har ya yi tauri.
5- Atisaye: Atisaye ko motsa jiki, na taimaka wa rage taurin bayan gida. Haka nan, atisaye na taimakawa wajen rage kiba, wanda hakan zai rage nauyi ko takura ga jijiyoyin jini a cikin dubura.
6- Kauce wa dogon zama: Dogon zama musamman yayin tsuguno, na kara takura jijiyoyin jini a dubura.
Haka zalika, Basir larura ce da ake warkewa sumul, bayan amfani da magunguna da sauran hanyoyi a likitance, amma idan Basir ya yi tsanani; yin tiyata na iya zama tilas ko wajibi.
Don haka, a tuntubi likita da zarar an fara jin alamomin Basir sun fara bayyana, maimakon shan magungunan gargajiya da ba a da tabbacin ingancinsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp