ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, October 26, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hanyoyin Kare Kai Daga Cutar Basir Cikin Sauƙi

by Sani Anwar
1 year ago
Basir

Cutar Basir da ake kira da ‘Hemorrhoids’ ko ‘Piles’ a turance, larura ce da ke ci gaba da shan gurguwar fahimta a tsakanin al’umma.

A likitance, ba wani abu ne Basir ba; face kumburarrun jijiyoyin jini a cikin karshen babban hanji da kuma dubura. Wadannan kumburarrun jijiyoyin jinin, su ne suke talewa har su yi bulli cikin karshen babban hanji ko kewayen dubura.

  • Koyo Daga Tarihi Da Kiyaye Zaman Lafiya Za Su Sa Kaimi Ga Zamanantar Da Duk Duniya Baki Daya
  • Maulidi: Gwamnan Zamfara Ya Taya Al’ummar Musulmi Murna, Ya Buƙaci A Dage Da Addu’o’in Samun Zaman Lafiya

Har ila yau, Basir a cikin karshen babban hanji shi ne, Basir cikin dubura, yayin da Basir a kewayen dubura kuma shi ne Basir wajen dubura.

ADVERTISEMENT

Haka nan, Basir mai tsiro; ci gaban Basir cikin dubura ne, wanda ke bayyana yayin da matsalar ta je matakin karshe. Basir mai tsiro, na faruwa ne sakamakon zazzagowa ko saukowar jijiyoyin jinin da suka yi bulli zuwa wajen dubura, musamman yayin yunkuri.

 

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Umarci Hukumomi Su Ƙarfafa Wayar Da Kai Kan Cutar Ebola

Ma’aikatan Lafiya Sun Janye Yajin Aikin Gargaɗi A Katsina

Alamomin Basir

Bayyanar alamomin Basir, ya danganta ga wane irin Basir ne ya bayyana, Basir cikin dubura ko kuma Basir a wajen dubura?

Alamomin Basir Cikin Dubura:

1- Zubar jini ba tare da jin ciwo ba, a yayin tsuguno.

2- Basir mai tsiro, wanda ke fitowa wajen dubura; har sai an tura da yatsa, domin mayar da shi. Yana haifar da ciwo da radadi.

Alamomin Basir A Wajen Dubura:

1- Ciwo mai radadi

2- Kaikayi

3- Kumburi a kewayen dubura

4- Zubar jini yayin yunkurin tsuguno

Abuban da ke kawo Basir: Basir na faruwa ne sakamakon takura jijiyoyin jini a dubura, har su kumbura sannan su yi bulli saboda abubuwa kamar haka:

1- Yawan yunkuri yayin tsuguno

2- Tsawaitar lokacin tsuguno

3- Fama da atini ko kuma taurin bayan gida tsawon lokaci

4- Kasancewa mai kiba ko teba.

5- Kasancewa mai juna biyu

6- Cin abincin mai karancin dusa, harza ko ganyayyaki

7- Daga nauyi akai-akai da sauran makamantansu

Hanyoyin Kiyaye Basir Cikin Sauki

Hanya mafi kyau wajen kiyaye kai daga basir ita ce, sanya bayan gida ya zamo mai taushi yadda zai fice ba tare da yunkuri sosai ba.

Wadannan hanyoyi, za su taimaka wajen kiyaye kai daga Basir da kuma rage matsalolinsa:

1- Cin abinci mai dusa sosai: Abinci mai dusa ya hada da ‘ya’yan itatuwa, ganyayyaki da kuma datsar hatsi.

2- Shan isasshen abin sha: Shan isasshen ruwa akalla lita biyu zuwa uku a kowace rana da sauran ababen sha masu ruwa-ruwa.

3- Rage yunkuri yayin tsuguno: Yunkuri tare da rike numfashi yayin tsuguno na takura jijiyoyin jini a cikin dubura.

4- Garzayawa da zarar jin bayan gida: Yin buris da bayan gida yayin da aka ji shi, na jawo jiki ya ci gaba da tsotse ruwan bayan gidan har ya yi tauri.

5- Atisaye: Atisaye ko motsa jiki, na taimaka wa rage taurin bayan gida. Haka nan, atisaye na taimakawa wajen rage kiba, wanda hakan zai rage nauyi ko takura ga jijiyoyin jini a cikin dubura.

6- Kauce wa dogon zama: Dogon zama musamman yayin tsuguno, na kara takura jijiyoyin jini a dubura.

Haka zalika, Basir larura ce da ake warkewa sumul, bayan amfani da magunguna da sauran hanyoyi a likitance, amma idan Basir ya yi tsanani; yin tiyata na iya zama tilas ko wajibi.

Don haka, a tuntubi likita da zarar an fara jin alamomin Basir sun fara bayyana, maimakon shan magungunan gargajiya da ba a da tabbacin ingancinsu.

Basir
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    MDPCO Ta Soki Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu A Kaduna
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Shirin Sulhu Tsakanin Kwankwaso Da Abba: Ina Aka Dosa?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya

MASU ALAKA

Gwamnatin Tarayya Ta Umarci Hukumomi Su Ƙarfafa Wayar Da Kai Kan Cutar Ebola
Kiwon Lafiya

Gwamnatin Tarayya Ta Umarci Hukumomi Su Ƙarfafa Wayar Da Kai Kan Cutar Ebola

October 23, 2026
Ma’aikatan Lafiya Sun Janye Yajin Aikin Gargaɗi  A Katsina
Kiwon Lafiya

Ma’aikatan Lafiya Sun Janye Yajin Aikin Gargaɗi A Katsina

October 19, 2026
Likitocin Ƙwaƙwalwa 250 Ne Kacal A Nijeriya, Ragowar Sun Gudu Ƙasashen Waje
Kiwon Lafiya

Likitocin Ƙwaƙwalwa 250 Ne Kacal A Nijeriya, Ragowar Sun Gudu Ƙasashen Waje

October 10, 2026
Next Post
Shawara Ga Matashin Da Matarsa Ta Samu Juna Biyu (1)

Shawara Ga Matashin Da Matarsa Ta Samu Juna Biyu (1)

LABARAI MASU NASABA

Wata Mata Ta Caka Wa Mijinta Wuƙa Kan Rigimar Wayar Salula A Bauchi

Wata Mata Ta Caka Wa Mijinta Wuƙa Kan Rigimar Wayar Salula A Bauchi

October 25, 2026
An Yi Taron Karawa Juna Sani Na Murnar Cika Shekaru 81 Da Maido Da Taiwan Kasar Sin A Birnin Fuzhou

An Yi Taron Karawa Juna Sani Na Murnar Cika Shekaru 81 Da Maido Da Taiwan Kasar Sin A Birnin Fuzhou

October 25, 2026
Nan Gaba Kaɗan Zan Bayyana Waɗanda Ke Daƙile Takarata – Pantami

Nan Gaba Kaɗan Zan Bayyana Waɗanda Ke Daƙile Takarata – Pantami

October 25, 2026
Xi Da Sarki Philippe Na Belgium Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Alakar Kasashensu

Xi Da Sarki Philippe Na Belgium Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Alakar Kasashensu

October 25, 2026
Mai Taimaka Wa Babban Sakataren MDD Ya Yaba wa Kasar Sin Bisa Hangen Nesanta

Mai Taimaka Wa Babban Sakataren MDD Ya Yaba wa Kasar Sin Bisa Hangen Nesanta

October 25, 2026
Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Manoma  2 A Wani Sabon Hari A Kaduna

Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Manoma 2 A Wani Sabon Hari A Kaduna

October 25, 2026
NCDC Za Ta Fara Biyan Mutanen Da Aka Killace ₦100,000 Saboda Ebola

NCDC Za Ta Fara Biyan Mutanen Da Aka Killace ₦100,000 Saboda Ebola

October 25, 2026
Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Na Intanet

Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Na Intanet

October 25, 2026
Farashin Tumatir Ya Tsiri, Na Barkono Ya Sauka A Legas

Farashin Tumatir Ya Tsiri, Na Barkono Ya Sauka A Legas

October 25, 2026
Jami’in WHO: Kasar Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Habaka Ci Gaban Magungunan Gargajiya A Duniya

Jami’in WHO: Kasar Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Habaka Ci Gaban Magungunan Gargajiya A Duniya

October 25, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.