A kan haifi jari da tawayar tafin sawu, sakamakon matsalolin da kan faru yayin rainon ciki ko tawayar cikar halitta da sauran makamantansu.
Daga cikin irin wadannan tawayoyi, akwai tawayar nadewar tafin sawu da ake kira da ‘Clubfoot’ a turance, wato tafin sawun na murdewa ko tankwarewa ciki, har ya yi kama da kan sandar gora.
- Layin Dogo Na Habasha-Djibouti Na Kara Karfin Jigilar Kayayyaki Zuwa Kasashen Waje
- Farashin Kayan Abinici Ya Karu Da Kashi 91.6 Cikin Shekara Daya -NBS
Kashi 80 cikin 100 na matsalar, na faruwa ne ga jarirai a kasashe masu matsakaici da mafi karancin tattalin arziki a duniya. Kazalika, kashi 50 cikin 100 na wannan matsala; na faruwa ne a tafukan sawu biyun.
Maza sun ninka mata sau uku wajen samun ire-iren wannan matsala.
Har ila yau, barin yaro da irin wannan matsala; na kawo matsaloli kamar haka;
1-Munin sifar tafin sawu
2-Ciwon tafin sawu
3-Wahalar tafiya
4-Wahalar zirga-zirga da tafiye-tafiye
5-Tsangwama da dai sauransu
Akwai hanyoyin gyara ko mikar da wannan tafin sawu ta hanyar amfanin da filasta tsawon mako hudu zuwa takwas. Wani lokacin kuma, ta kan kai ga yin tiyata idan matsalar ta yi matukar ta’azzara.
An fi samun nasarar gyaran tafin sawun yadda ya kamata, idan aka fara yin gyaran kafin yaro ya fara tafiya. A likitance, ana ayyana cewa; an yi buris da gyaran tafin sawu idan yaro ya wuce shekara biyu ba a gyara ba. Kazalika, daukar tsawon lokaci ba tare da yin gyaran tafin sawun ba, na nuni ko barazana da raguwar nasarar gyaran.
Saboda haka, da zarar an lura yaro ya zo da irin wannan matsala, sai a yi sauri a tuntubi likita; don kauce wa irin wannan nakasa ta nadewa ko tankwarewar sawu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp