Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Adon Da Kwalliya.
Domin kula da lafiyar gabanki, ta yadda za ki kasance da kyau kuma ki dawwama da ni’ima na gamsar da maigida a duk lokutan yin Jima’inku. To ki kasance duk jima’in da za ku yi kuna gamawa ki yi wadannan abubuwan kamar haka:
Abu na farko da za ki rinka yi shi ne; ki soma yin fitsari.
Yin fitsari bayan kammala jima’i ya kan taimakawa mace kariya da fitar da duk wasu kananan halittun da suka shige ta, fitar da su ta hanyar yin fitsarin. Sannan idan kin je yin fitsarin kada ki sako shi lokaci guda a hankali za ki yi shi. Kina yi kina matsewa da haka har ki kammala har sai kin ji mararki babu sauran fitsarin, sannan kuma ki tabbatar kin yi tsarki da ruwa mai dumi ba mai sanyi ba.
Yin amfani da ruwan dumi ya kan taimaka wa mace gabanta ya koma yadda yake, haka kuma ruwan dumi ya kan halaka duk wasu cututtuka da suka nemi shiga gabanta, tsarki da ruwan dumi bayan kammala jima’i yana magance fitar iska ta gaban mace, hakan ya sa yake da kyau uwargida ta kula.
Ki tabbatar kin wanke hannunki da kyau kafin ki fito a bayan gidan.
Yin hakan yana kashe duk wasu cututtukan da aka dauka ko za’a dauka cikin yatsu ko hannu. A lokacin jima’i ko wasannin motsa sha’awa ma’aurata na amfani da hannu ko yatsunsu wajen yi wa juna wasa, a irin hakan ana iya samun cewa kwayar cuta ta makale ta hakan sai a sake fitowa da ita maimakon rabuwa da ita a lokacin da aka shiga tsaftace jiki, don haka ki tabbatar kin tsaftace hannuwanki da yatsunki tsaf kafin ki fito.