ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, November 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hanyoyin Tsuke Gaba Wato Matsi?

by Bilkisu Tijjani
12 months ago
Gaba

Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Ko Kin San.

A yau shafin na mu zai kawo muku abubuwan da mata za su yi domin matse gaba.

  • Ana Ci Gaba Da Neman Wadanda Suka Bace Bayan Kifewar Jirgin Ruwa A Masar
  • Sin Ta Yi Tir Da Matakin Amurka Na Sayarwa Taiwan Makamai

Akwai hanyoyi da dama na matse gaba musamman bayan haihuwa wanda suka hada da hanyoyin magani, motsa jiki (edercise), tiyatar likita domin rage girman gaba da sauransu. Wasu hanyoyin na da illa ga lafiya, wasu kuma hanyoyin ba su da wata matsala ko hadari kamar dai yadda likitoci ke bayani.

ADVERTISEMENT

Wasu daga cikin hanyoyin:

Na daya: Kamar yadda Ibrahim Y. Yusuf ya fara fada, motsa jiki, hanyoyin motsa jiki na zamani domin matse gaban mace suna da yawa, wato motsa jiki wanda ake yi a kwance rigingine ana daga kafafu. Motsa jikin ya shafi horo da mace za ta iya ba wa jikinta. Matan dake motsa jikinsu yana kara karfi da tsukewa. Misali, wata kwararriyar likita a Indiya Dr. Sangeeta Gomes, ta nuna cewa mace za ta iya inganta tsukewar gabanta idan tana motsa jikin dauke numfashi.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Za Ku Gyara Kanku

Maganin Nankarwa (4)

Za ki dauke numfashinki na tsawon ‘yan dakikoki kadan sannan ki tsuke (tsokokin) farjinki, matakan na tsawon wani lokaci a lokacinda kike mai dauke numfashin. Za ki yi hakan a kowace rana, sau 10 ko 15. Za ki iya yin hakan a kicin lokacin da kike aiki, a ofis, a tsaye ko a zaune, a ko ina kuma a ko wane wuri ba tare da ma wani ya san abin da kike yi ba. Sa’annan za ki yawaita cin ‘ya’yan itatuwa wato (kayan marmari) da abincin ganye.

Wannan ko shakka babu zai taimakawa mace wajen matse gaba domin gyara aurenta. Wani nau’in motsa jikin kuma shi ne ake kira da “Kegel edercise”. To  yaya ake yin sa? Dr. Gomes ta nuna cewa idan kina yin fitsari sai ki tsaida fitar fitsarin, wato ki  rike fitsarin, ki danne shi na tsawon dakikoki 10, wato ki kirga 1 zuwa 10 sa’annan ki saki fitsarin a hankali a hankali. Za ki iya yin hakan sau 2 ko 3 a rana idan za ki yi fitsari. Shima wannan nau’in motsa jikin na tsuke gaban mace ne.

Na Biyu. Hanya ta biyu ita ce, wanke gaba da ruwan sanyi mai kankara. Yana taimakawa wajen matse gaba, amma sai an hada da motsa jikin da muka yi bayani. Wannan yana daga cikin hanyoyin da Dr. Gomes ta zayyana, amma zai fi dacewa a ce sai mace ta gama wankan jegonta na kwana 40 kwatakwata sa’annan ta yi amfani da ruwan sanyin, wato bayan ta koma “normal”, sabanin yadda al’adar Bahaushe ta yi imani da shi cewa ruwan sanyi na lalata gaban mace, wasu likitocin a wasu al’adun na ganin yana matse gaba.

Na uku: Yin amfani da aluf (alum). Aluf yana matse gaba sosai sai dai likitoci na tsoratarwa akan yin hakan saboda da sinadarin kemikal ne.

Na Hudu: Yin tiyatar likita domin rage budewar farji. Wannan ma hanya ce ta zamani amma ana tsoratarwa akan yin hakan saboda wasu dalilan lafiya.

Na Biyar: Yunkurin tsuke gaba a lokacin saduwa, wato ki matse farjinki ta ciki lokacin da mijinki yake kai-kawo. Za ki yawaita yunkuri domin tsuke gabanki domin mijinki ya ji alamun ana rike masa al’aura tamkar zobe zagayen gabansa. Idan mace na yawaita yin da haka to zai zama dabi’arta kuma nan gaba ba za ta san ma tanayin hakan ba saboda ta riga ta horar da jikinta, kuma hakan zai inganta jin dadin mijinta sosai. Allah Ya taimaka.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Za Ku Gyara Kanku
Ado Da Kwalliya

Yadda Za Ku Gyara Kanku

November 15, 2025
Maganin Nankarwa (4)
Ado Da Kwalliya

Maganin Nankarwa (4)

November 8, 2025
Yadda Za A Magance Amosanin Baki
Ado Da Kwalliya

Yadda Za A Magance Amosanin Baki

October 4, 2025
Next Post
Talauci Ya Sa Ake Samun Karuwar Matasa Masu Fasahar Waka A Nijeriya -Tiwa Savage

Talauci Ya Sa Ake Samun Karuwar Matasa Masu Fasahar Waka A Nijeriya -Tiwa Savage

LABARAI MASU NASABA

Yadda Za A Magance Yawan Faɗace-faɗace A Wasannin Gasar Firimiyar Nijeriya

Yadda Za A Magance Yawan Faɗace-faɗace A Wasannin Gasar Firimiyar Nijeriya

November 16, 2025
Kwankwaso

NNPP Tana Da Ƙwarin Gwiwar Riƙe Kano Da Lashe Jihohin Arewa A Zaɓen 2027 – Ajuji

November 16, 2025
Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna?

Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna?

November 16, 2025
Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan

Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan

November 15, 2025
Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca

Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca

November 15, 2025
Sin Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Matakin Amurka Na Ingiza Daftarin Tsawaita Aikin Tawagar UNISFA 

Sin Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Matakin Amurka Na Ingiza Daftarin Tsawaita Aikin Tawagar UNISFA 

November 15, 2025
Za A Yi Gwanjon Rigunan Messi Na Gasar Kofin Duniya Ta 2022 Da Kudi Tsagwagwa

Ina Son Kasancewa Cikin Koshin Lafiya Kafin Buga Gasar Kofin Duniya Na Shekarar 2026 – Messi

November 15, 2025
Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Gina Sabbin Ginshikan Samar Da Ci Gaban Kasa Masu Inganci

Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Gina Sabbin Ginshikan Samar Da Ci Gaban Kasa Masu Inganci

November 15, 2025
Duk Niyyar Da Mutum Ya Shigo Da Ita Kannywood Ita Za Ta Bi Shi —HAUWA KUJAMA

Duk Niyyar Da Mutum Ya Shigo Da Ita Kannywood Ita Za Ta Bi Shi —HAUWA KUJAMA

November 15, 2025
Sin Ta Sha Alwashin Bunkasa Goyon Bayan Juna Tsakaninta Da Saliyo

Sin Ta Sha Alwashin Bunkasa Goyon Bayan Juna Tsakaninta Da Saliyo

November 15, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.