Jiya Laraba 11 ga wata ne, ministan harkokin wajen kasar Sin wanda a yanzu haka yake ziyara a nahiyar Afirka, Qin Gang, da shugaban hukumar gudanarwar kungiyar AU, Moussa Faki Mahamat, suka halarci shawarwarin Sin da AU karo na 8, gami da bikin kammala ginin babbar hedikwatar cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Afirka.
Game da wannan ziyara, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin, Wang Wenbin ya bayyana a yau Alhamis cewa, har kullum kasar Sin na baiwa kasashen Afirka fifiko, a yayin da take gudanar da harkokin diflomasiyya, kana, gado gami da yaukaka zumuncin bangarorin biyu, ya zama wata muhimmiyar al’ada cikin harkokin diflomasiyyar kasar Sin.
Kakaki Wang ya ce, gina babbar hedikwatar cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa ta Afirka, gagarumin aikin hadin-gwiwar Sin da Afirka ne, wanda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar, a wajen taron kolin dandalin tattauna hadin-gwiwar Sin da Afirka da aka yi a shekara ta 2018 a birnin Beijing, kana, wani muhimmin aiki ne na daban, dake shaida hadin-gwiwar bangarorin biyu, ban da babbar cibiyar taro ta kungiyar AU. Minista Qin ya bayyana cewa, Sin kasa ce dake cika alkawuranta, kuma ba za ta tilastawa sauran kasashe yin wani abu ba. Yanzu Sin ta yi nasarar mika babbar hedikwatar cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa ta Afirka ga ‘yan uwanta na Afirka, wadda kungiyar AU za ta karbi ikonta kwata-kwata. Wannan wata babbar nasara ce da aka cimma, sakamakon dadadden zumunci dake tsakanin al’ummomin Sin da Afirka, gami da jajircewarsu wajen aiki. Qin ya ce, in dai Afirka na da bukata, kasar Sin za ta yi iya kokarinta don ci gaba da samar da goyon-baya da taimako gare ta. (Murtala Zhang)