Da duk mai bibiyar al’amuran dake gudana a sassan duniya musamman a ’yan kwanakin nan, ba zai rasa jin rahotanni game da yadda wata girgizar kasa mai karfin maki 6.2 ta auku a gundumar Jishishan ta lardin Gansu na kasar Sin ba, lamarin da ya haifar da rasuwar sama da mutane 130, tare da jikkatar wasu karin mutanen da dama.Â
Wannan lamari ya girgiza duniya, tare da sanya al’ummun kasa da kasa cikin yanayi na alhini. Kuma sassan kasashen duniya na ta kara aikowa gwamnatin Sin sakwannin jaje, da ta’aziyya, bisa aukuwar wannan ibtila’i.
- Shugaban Kasar Sin Ya Gana Da Firaministan Kasar Rasha
- Sin Ta Kara Tallafin Kudi Don Maido Da Wuraren Kiyaye Ruwa A Yankunan Da Girgizar Kasar Ta Shafa
Sai dai duk da halin alhini da Sin din ke ciki na aukuwar wannan girgizar kasa, mahukuntanta ba su manta da aniyarsu ta taimakawa sauran sassa dake cikin makamancin wannan yanayi ba, inda a ranar Talata ma jakadan kasar Sin a kasar Somalia, ya mikawa gwamnatin kasar tallafin dalar Amurka miliyan daya, a matsayin taimakon jin kai bisa bala’in ambaliyar ruwa da ya auku a kudanci, da yankin tsakiyar kasar dake kahon Afrika, sakamakon tasirin sauyin yanayi na El Nino, wanda kuma hakan ya haifar da rasuwar sama da mutane 100, tare da raba mutane miliyan daya da dubu dari bakwai da muhallansu.
Ko shakka babu, wannan mataki ya nuna yadda Sin ke sauke nauyin dake wuyanta a matsayin kasa mai tasowa mafi girma a duniya, wadda har kullum ba ta kasa a gwiwa wajen tallafawa, da goyon bayan sauran ’yan uwan ta kasashe masu tasowa a kowane hali.
Wannan abun alheri da Sin ta gabatar ga Somaliya a irin wannan lokaci mawuyaci, ya ja hankalin masharhanta, baya ga su kansu alummar Somalia, dake cewa Sin din ce kasa ta farko da ta samar musu da tallafin jin kai tun bayan aukuwar wannan ibtila’i na ambaliyar ruwa.
A cewar wasu majiyoyi daga Somalia, wannan ne karo na 4 da Sin ta tuntubi kasar game da ayyukan tallafin jin kai a cikin shekarar bana kadai, wanda hakan ke shaida ingancin dadadden zumunci da tarihin kawance dake wanzuwa tsakanin Sin da Somalia.
Yayin da muke fatan sauki daga irin wadannan bala’u a dukkanin sassan duniya, tarihi ba zai taba mantawa da yadda Sin ke nacewa manufarta ta tallafawa abokan tafiya, kasashe masu tasowa musamman na nahiyar Afirka ba. (Saminu Alhassan)