Awanni 48 bayan sace ƴan jarida biyu da iyalansu a Jihar Kaduna, har yanzu ba a san inda suke ba. ‘Yan bindiga sun kutsa cikin unguwar Danhonu a Millennium City, ƙaramar hukumar Chikun, inda suka kai hari gidajen AbdulGafar Alabelewe na jaridar The Nation da AbdulRaheem Aodu na jaridar Blueprint, suka sace su tare da matansu da ‘ya’yansu. An sako matar AbdulRaheem daga baya saboda rashin iya bin masu sacewa sakamakon rashin lafiya.
Ɗan uwa ga ɗaya daga cikin waɗanda aka sace, Taofeeq Olayemi, ya bayyana damuwar da iyalan suke ciki, yana mai cewa ba su samu wata alaƙa da ‘yan uwan da aka sace ba tun bayan faruwar lamarin ba. Ya ce, “Wannan lokaci ne mai matuƙar wahala ga iyalan saboda ba mu san halin da suke ciki ba kuma ba mu san inda suke ba. Muna ta addu’a ga Allah ya kiyaye su kuma ya sassauta zuciyar waɗanda suka sace su.”
- Ƴancin Ƙananan Hukumomi Zai Taimaka Wajen Magance Matsalolin Tsaro – COAS
- Atiku Ya Koka Kan Yadda Matsalar Tsaro Ta Addabi ‘Yan Nijeriya
Kakakin rundunar ‘yan sanda (PPRO) a Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya ce jami’an tsaro suna iyakar kokarinsu don ganin sun kuɓutar da waɗanda aka sace ba tare da wani rauni ba. Ya bayyana cewa an tura jami’ai cikin dajin da ake zaton ‘yan bindigar suke buya.
Ƙungiyar ‘Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ) a Kaduna ta yi tir da wannan sacewa a cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Comrade Asmau Yawo Halilu, da Sakataren ƙungiyar, Comrade Gambo Santos Sanga, suka sanya wa hannu. Sun roƙi hukumomin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa don ceto ‘yan jaridar da iyalansu.
Kungiyar Arewa Youth Consultative Forum (AYCF) ta yi Allah wadai da garkuwar da aka yi da ƴan jaridar. Shugaban ƙungiyar, Alhaji Yerima Shettima, ya yi kira ga hukumomin gwamnati da na tsaro su ƙara kokari don ganin an sako waɗanda aka sace lafiya kuma a kawo karshen irin waɗannan munanan al’amura. Ya kuma bukaci jama’a su yi addu’a don ganin an sako waɗanda aka sace lafiya.