Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaryata jita-jitar da ke cewa zai bar jam’iyyar PDP domin komawa jam’iyyar APC mai mulki ko sabuwar jam’iyyar haɗakar adawa ta ADC. Ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television a daren Laraba.
Gwamna Lawal ya ce har yanzu mamba ne na jam’iyyar PDP kuma bai da wani shiri na sauya sheƙa. Ya ce duk wata jita-jita da ake yaɗawa cewa ya shirya komawa APC ko wata jam’iyya daban, ba gaskiya ba ce. “Ni har yanzu ina cikin PDP kuma babu inda zan je yanzu,” in ji shi.
- Zamfara Babban Wuri Ne Na Aikin Noma Mai Amfani Da Hasken Rana – Gwamna Lawal
- Na Biya Bashin Garatutin Naira Biliyan 13.6 Da ’Yan Fanshon Zamfara Ke Bi Tun 2011 – Gwamna Lawal
Ya ce dukkanin masu adawa da shi a jihar sun tsaya a zaɓen 2023, amma hakan bai hana shi nasarar lashe zaɓen gwamna ba. Ya ƙara da cewa bai jin tsoron tsoffin gwamnoni irin su Sani Yerima, da Bello Matawalle da Abdulaziz Yari, yana mai cewa zai sake kayar da su a 2027 idan suka tsaya takara.
Gwamnan ya amince cewa PDP na fuskantar wasu rikice-rikice na cikin gida, amma ya ce jam’iyyar na aiki tuƙuru wajen warware matsalolin kuma lokaci nan kusa da komai zai daidaita.
Dangane da dangantakarsa da Shugaba Bola Tinubu, Lawal ya ce suna da kyakkyawar mu’amala, duk da cewa suna jam’iyyu daban. Amma dangane da goyon bayan shugaban ƙasa a zaɓen 2027, ya ce lokaci zai bayyana komai, domin yanzu bai dace a maida hankali ga siyasa ba, sai a fi mai da hankali kan shugabanci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp