Ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya yi ikirarin cewa har yanzu shi mamba ne a jam’iyyar adawa ta PDP da ke aiki a gwamnatin APC mai mulki.
Wike ya bayyana haka ne a cikin shirin gidan talabijin na Channels a daren ranar Laraba.
- Gwamnatin Kaduna Ta Fara Rabon Kayan Aiki Ga Cibiyoyin Kiwon Lafiya 290
- Gidajen Wanka Sun Kara Kudin Ba-Haya A Kano
Ya nanata cewa shi dan jam’iyyar PDP ne amma yana aiki tare da shugaban kasa Bola Tinubu domin cimma manufofinsa.
Wike ya kuma bayyana cewa gwamnonin PDP sun rubuta wasiku ga shugaba Tinubu, inda suka zabi abokansu domin gwamnatin APC ta nada su.
Ya ci gaba da cewa ya samu izinin jam’iyyar PDP kafin ya amince da nadin mukamin minista da APC ta yi masa.
Wike, ya bayyana cewa ya rubuta wa shugabannin jam’iyyar PDP a matakin shiyyar Kudu-maso-Kudu da Jihar Ribas kawai, wadanda su kuma suka nemi ya amince da nadin ministan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp