Asusun bayar da lamuni na duniya (IMF) ya bayyana cewa gwamnatin Nijeriya karkashin Shugabancin Bola Ahmed Tinubu tana bayar da tallafin man fetur ta bayan fage.
Idan dai za a iya tunawa tun a ranar 29 ga Mayun 2023 lokacin da Shugaban kasa Tinubu yake jawabinsa na farko ya bayyana cire tallafin man fetur, wanda hakan ya haddasa tsadar farashin kayayyaki a cikin kasar nan.
- Nijeriya Za Ta Shawo Kan Ƙalubalen Da Take Fuskanta Nan Gaba Kaɗan – Ganduje
- Shugaba Tinubu Ya Gana Da Gwamnoni Kan Ƙalubalen Da Nijeriya Ke Fuskanta
Bayan wasu ‘yan makonni, Babban Bankin Nijeriya ya rushe tsarin canjin kudaden waje zuwa na bai daya tare da karya darajar naira, wanda hakan ya janyo darajar naira da karye.
A wannan makon ne IMF ya shawarci gwamnatin tarayyar Nijeriya kan ta cire tallafin mai da na wutar lantarki gaba daya.
Sai dai kuma wannan shawara ya hadu da suka a wurin wasu ‘yan Nijeriya wadanda suke ganin a halin yanzu ma ana farama da matsin rayuwa ballantana an sake cire tallafin mai da kuma na wutar lantarki, inda suke ganin cewa idan har gwamnati ta amince da wannan shawara, to za a shiga mawuyacin halin da ba a taba shiga a Nijeriya ba.
A kwanakin baya ne wasu rahotanni suka bayyana cewa an samu dogayen layuka a gidajen man fetur a wasu manyan buranin kasar nan, amma kuma kamfanin mai na kasa (NNPC) ya bayyana wa ‘yan kasar cewa akwai isasshen man fetur.
Bayan cire tallafin man fetura a watan Mayun 2023, farashin litar man fetur ta tashi daga naira 185 zuwa 400, yayin da daga baya a gidajen mai na NNPC ake sayar da shi kan naira 568, sauran gidajen man kuma ana sayar da shi ne kan naira 600.
Gwamnati ta bayyana cewa farashin man zai ci gaba da sauyawa lokaci bayan lokaci bayan cire tallafin man, amma kuma litar man zai tsaya yadda yake duk da sauyawan farashin danyan mai a kasuwar duniya, wanda yake iya hawa da kuma sauka.
IMF ta ce muddin gwamnatin Tinubu ta ci gaba da biyan tallafin man fetura da na wutar lantarki, zai ci gaba da janyo hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa.
Wani bincike ya tabbatar da cewa duk da irin ikirarin Shugaba Tinubu na cire tallafin man fetur, gwamnatin tarayya ta biya tallafin naira biliyan 169.4 a watan Agustan baya domin farashin litar man ya ci gaba da zama kan naira 620.
Sai dai kuma sau uku dillalan man fetur suna kara farashin litar a tsakanin watan Agusta zuwa Disambar 2023, inda lamarin ya tilasta musu sayar da litar man kan tsakanin naira 660 zuwa 670.
Amma gidajen mai na NNPC na ci gaba da sayar da litar man kan naira 617. Yayin da suka gidajen mai na ‘yan kasuwa har sun fara sayar da litar man kan naira 720 a wasu wurare.