Ma’aikatar kula da cinikayya ta kasar Sin ta ce taruwar harajin Amurka kan kayayyakin Sin ba za ta bayar da gudunmuwa ga ikirarin tsaron kasa na Amurka ba, haka kuma ba za ta taimakawa masana’antun cikin gidan kasar ba. Abun da kawai take nunawa shi ne, dabi’ar Amurka ta aiwatar da ra’ayi na kashin kai da kariyar cinikayya da cin zali.
Kakakin ma’aikatar He Yongqian ce ta bayyana haka, lokacin da aka nemi jin ta-bakinta game da karin harajin Amurka kan kayayyakin Sin, yayin wani taron manema labarai a yau Alhamis.
- Tabbaci Kan Bunkasuwar Tattalin Arziki Mai Dorewa A SinTabbaci Kan Bunkasuwar Tattalin Arziki Mai Dorewa A Sin
- Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [5]
A cewar kakakin, ko ana batun haraji mai lamba 301 ko mai lamba 232, tsarin warware takaddama na hukumar kula da cinikayya ta duniya WTO, ya riga ya ayyana dukkansu a matsayin wadanda suka keta dokokin cinikayya ta kasa da kasa.
A cewar kakakin, kasar Sin ta sha nanata cewa, wadannan haraji da ake kakabawa da sunan tsaron kasa, wani tsari ne na kariyar cinikayya da aiwatar da ra’ayi na kashin kai. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp