Hedikwatar Tsaro (DHQ) ta bayyana cewa harin jirgin sama da ta kai a Sakkwato, ta kai ne da hallaka ‘yan ta’addan Lakurawa tare da wajen ajiyar kayan aikinsu.
Sia dai harin ya yi sanadin mutuwar fararen hula a jihar.
- Turmutsutsin Rabon Kayan Tallafi: Alama Ce Na Yadda Gwamnatin APC Ta Jefa ‘Yan Nijeriya Cikin Talauci – PRP
- Sojoji Sun Kashe Shugaban Ƴan Ta’adda A Zamfara
Daraktan Yada Hulɗa Labarai na Rundunar, Manjo Janar Edward Buba, ya ce an tsara aikin sosai ta amfani da bayanan sirri da leƙen asiri inda aka tabbatar da wajen sansanin ‘yan ta’adda ne.
Ya kuma jaddada cewa an kai harin ne cikin taka-tsan-tsan don rage yiwuwar cutar da fararen hula.
Buba, ya bayyana cewa harin jirgin ya auku da sassafe a ranar 25 ga watan Disamba, 2024, inda ya kai ga fashewar wasu abubuwa a sansanin maharan.
Rundunar sojojin ƙasa ta tabbatar da cewa an lalata sansanin ‘yan ta’addan tare sai dai abubuwan da suka fashe sun ti lahani ga ƙauyukan da ke kewaye.
Sojojin sun kuma tabbatar da cewa wasu daga cikin ‘yan ta’addan sun tsere bayan harin, yayin da wasu suka mutu.
Mazauna yankin sun tabbatar da cewa ‘yan ta’addan Lakurawa sun yi amfani da wajen a matsayin sansaninsu.
Janar Buba ya tabbatarwa da jama’a cewa rundunar sojoji ta ɗauki matakai don kauce wa asarar rayukan fararen hula.
Ya kammala da cewa burin sojoji shi ne su kawar da ‘yan ta’adda, ba tare da cutar da fararen hula ba.