Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya kaddamar da gini tare da hanya mai tsawon kilomita 5.5 zuwa garin Tudun Biri da ya fuskanci harin Bam daga jirgi mara matuki na sojoji a watan Disambar 2023.
Haka kuma, za a gina cibiyar koyar da sana’o’i da cibiyar kula da lafiya matakin farko na zamani domin yi wa Tudun Biri hidima da sauran kauyukan da ke makwabtaka da su da wannan mummunan harin ya rutsa da su.
- Harin Tudun Biri: Gwamnatin Kaduna Da ANRiN Sun Raba Kayan Abinci Da Irin Noma Ga Magidanta 100
- Gwamnatin Kaduna Ta Karɓi ‘Yansanda Masu Horo Na Musamman 200 Da Motocin Yaƙi 2
Idan dai za a iya tunawa, a sakamakon harin, gwamnan ya yi alkawarin gina tituna, makarantu, asibitoci, da sauran ayyukan raya kasa a tsakanin al’ummar.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da ginin a ranar Talata, Gwamna Sani ya ce, ayyukan za su bude hanyoyin kasuwanci ga manoma inda za su iya sayar da amfanin gonakinsu cikin sauki.