Mataimakin Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Idi Barde Gubana, ya ziyarci asibitin jihar domin jajanta wa wadanda harin Boko Haram ya rutsa da su a lokacin da suke dawowa Damaturu, babban birnin jihar.
Mutanen da suka samu raunuka daban-daban an kwantar da su a asibitin kwararru na Janar Sani Abacha da ke Damaturu domin kula da lafiyarsu.
- APC Na Amfani Da Kotu Wajen Murkushe Jam’iyyun Adawa – Atiku
- Zaben Nasarawa: ‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaro Gabanin Hukuncin Kotun Daukaka KaraÂ
Mataimakin gwamnan ya umarci babban daraktan kula da lafiya da tabbatar da an kula da wadanda lamarin ya shafa.
Barde Gubana ya yaba da jajircewar da ma’aikatan asibitin suka yi na bayar da agajin ga wadanda abin ya shafa.
Daga nan ya yi addu’ar samun sauki ga jami’an tsaron da harin ya rutsa da su.
Ya kuma yi ta’aziyya ga iyalan dan sandan da ya rasa ransa a yayin harin.
Mataimakin gwamnan ya samu tarba daga Dokta Usman Abba Geidam, wanda shugaban ma’aikatan lafiya Dokta Mohammad Aji ya wakilta, wanda ya ce ana kula da wadanda lamarin ya shafa yadda ya kamata.