Kwanaki 85 kenan da sace fasinjojin jirgin Abuja zuwa Kaduna, kimanin mata 50, yara da maza na cigaba da zama a tsare a mafakar ‘yan bindigan dake cikin dazuka.
Rahotannin sun nuna cewa sakamakon Ruwan sama da ake tafkawa, Macizai da Kunamo sun harbi wadanda suke tsaren, Mutum 9 daga cikinsu sun mutu sakamakon harbin da kuma mawuyacin halin da suke Ciki.
Hakan ya fito ne ta bakin mai baiwa Sheikh Ahmad Gumi shawara kan harkokin yada labarai, Malam Tukur Mamu, wanda ya shiga tsakani wajen ganin an sako fasinjoji 11 daga cikin fasinjojin jirgin da aka sace kwanan nan.
Mamu ya ci gaba da cewa galibin wadanda harin jirgin kasan ya rutsa da su, da kyar za su iya rayuwa nan da ‘yan makonni masu zuwa saboda tabarbarewar yanayin kiwon lafiyarsu da kuma mawuyacin halin da suke fuskanta a dajin.
Mamu ya jaddada cewa dole ne a dauki matakin ceton su idan gwamnati na son yawancinsu su dawo da rai.