Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Ahmed Idris Wase, ya bayyana cewa, kafin faruwar harin ‘yan ta’adda na fasa gidan yarin Kuje da ke Abuja, sai da hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta gabatar da rahotonnin tsaro har guda 44.
Idan za a iya tunawa, a ranar 5 ga watan Yulin 2022 ne, ‘yan ta’adda suka farmaki gidan yarin Kuje, inda suka saki fursunoni sama da 800 ciki har mayakan Boko Haram da ake tsare da su.
- Yajin Aikin ASUU: NLC, ASUU da Sauran Kungiyoyi Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Lumana A Kebbi
- NNPP Ga Buhari: Ka Sanya Dokar Ta Baci A Jihohin Arewa 5
Wase, ya bayyana hakan ne a lokacin da ke tofa albarkacin bakinsa dangane da kudurin neman haramta sana’ar Acaba a fadin kasar nan da gwamnatin tarayya ke da niyyar yi.
Kudirin wanda Hon. Abubakar Makki Yelleman (APC Jigawa) ya gabatar a zaman majalisar na ranar Talata.
Wase ya kara da cewa, “DSS sun gabatar da rahotonnin har guda 44 kafin harin Kuje ya auku. Na fada, kuma na tabbatar muku, na bibiyi dukkanin rahotonnin guda 44 kuma dukkaninsu su na da alaka da wannan.”
Wase ya ce akwai bukatar a tallafa wa yunkurin gwamnati na dakile aniyar ‘yan bindiga a cikin al’umma.