Ƙungiyar Arewa Consultative Forum (ACF), ta bayyana harin bam da aka kai a ranar Kirsimeti a Silame da ke Jihar Sakkwato, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 10 tare da jikkata wasu da dama, a matsayin “kuskuren da ba za a yarda da shi ba.”
Sojojin sun bayyana cewa harin ya nufi lalata kayan aikin ‘yan ta’adda, amma fashewar bam da ta biyo baya ce ta yi sanadiyyar mutuwar mutane.
- Ɓarayin Wutar Sola Sun Baƙunci Lahira Yayin Da Suke Tsaka Da Kwancewa
- Shugaba Xi Ya Mika Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Tsohon Shugaban Amurka Jimmy Carter
Sai dai, ACF ta soki wannan bayani, inda ta bayyana cewa hakan ya nuna rashin tausayi, tare da kiran a gudanar da bincike tare da fitar da sakamakon ga jama’a.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ta, Farfesa Tukur Muhammad-Baba, ya fitar, ACF ta miƙa ta’aziyya ga iyalan mamatan da gwamnatin jihar Sakkwato, tare da kira ga gwamnatin tarayya da sojoji su tabbatar da cewa irin wannan al’amari ba zai sake faruwa ba.
Haka kuma, ƙungiyar ta buƙaci a biya diyyar waɗanda suka rasa rayuka ko suka ji rauni bisa tanade-tanaden shari’ar Musulunci, tare da ba su tallafi.
Ƙungiyar ta jaddada goyon bayanta ga ƙoƙarin sojoji na yaƙi da ta’addanci, amma ta ce irin waɗannan “kurakurai ba za a aminta da su ba” sannan suna da matuƙar muni.
ACF ta kuma yi kira ga ƙungiyoyin agaji da masu hannu da shuni su taimaka wa iyalan da abin ya shafa a wannan mawuyacin lokaci.