Gwamna jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya bayyana cewa, nan da makonni biyu masu zuwa, za a fara sake gina garin Tudun Biri da wani jirgin soja mara matuki ya jefa wa Bam a ranar 3 ga watan Disamba, 2023.
Gwamnan ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Asabar din da ta gabata yayin da yake jawabi a wajen taron kwamitin zartarwa da ayyuka na kasa na kungiyar Fityanul Islam ta Nijeriya, wanda aka gudanar a jami’ar jihar Kaduna.
- Hunturu: Gidauniya Ta Tallafa Wa Masu Larurar Amosanin Jini 300 Rigunan Sanyi A Kaduna
- Zan Bar Barcelona A Karshen Kakar Wasanni Ta Bana-Xavi
Gwamnan Uba Sani ya yi alkawarin bayar da filayen gina Jami’ar da kungiyar Fityanul Islam ta Nijeriya ke shirin yi.
Da yake mayar da martani ga kalaman jagoran kungiyar Musulunci ta kasa wanda tun farko a jawabinsa ya bukaci a gaggauta cika alkawuran da aka dauka wa al’ummar Tudun Biri, Gwamna Sani ya ce, ya gana da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu kwanaki biyar da suka gabata kan alkawurran da gwamnatin tarayya ta dauka na sake gina garin Tudun Biri.
Ya ba da tabbacin cewa, za a gina gidaje, asibiti, makaranta, kasuwa da ofishin ‘yansanda a garin a karkashin aikin sake gina Tudun Biri da Gwamnatin Tarayya za ta yi.