Rundunar ‘yansandan Nijeriya reshen Jihar Kebbi, ta kwato wani makamin roka guda daya da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka yi watsi da su a kauyen Dan-Umaru da ke gundumar Bena a Karamar Hukumar Danko-Wasagu ta jihar.
Bayan samun wannan bayanin ne tawagar ‘yansanda daga sashen ‘yansanda na Dan-Umaru, suka ma-yar da martani cikin gaggawa da ruwan harsashi.
- Kotu Za Ta Yanke Hukunci Kan Shari’ar Wani Limami A Abuja Da Sanata Ndume 6 Ga Satumba
- An Kaddamar Da Shirin Baje Kolin Inganta Harkar Noma Da Sana’o’i A Kano
Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Samuel Titus Musa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Birnin Kebbi, yayin da yake gabatar da wadanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban a shalkwatar rundu-nar jihar.
Kwamishinan ya ce “Tawagar ‘yansandan sun yi nasarar dakile harin tare da gano makamin roka guda daya, da ‘yan bindigar da ake zargin sun tsere da raunukan harbin bindiga daban-daban.
Haka kuma ya kara da cewa, wani Aminu Bello dake Unguwar Almasira a cikin garin Jega, ya karbo bash-in Naira 485,000 daga abokinsa Abdulmajid Nasiru. Wanda ake zargin, Aminu Bello ya yaudari wanda abin ya shafa ya ja shi zuwa cikin wani daji da ke kusa da su inda ya daba masa wuka a wuya.
Sakamakon haka, wanda aka daba wa wukar ya fadi a sume kuma aka garzaya da shi babban asibitin Aisha Muhammadu Buhari da ke Jega inda wani likita da ke bakin aiki ya tabbatar da rasuwarsa. Daga nan sai jami’an ‘yansanda suka kama wanda ake zargin wanda ke shirin tserewa.
A yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa. A cewar kwamishinan ‘yansanda, bayan an kammala bincike za a gurfanar da shi a gaban kuliya.
Hakazalika, an kama wata mata Mai suna Hauwa Sulieman dake kauyen Babbar Dogo dake karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara, tana rike da harsashi harsashi guda dari biyar da sittin da shida (566) 7. 62×39mm. Ana gudanar da bincike kan lamarin. Da yake jaddada cewa an kama ta ne a yankin na kara-mar hukumar Danko-Wasagu a ranar 24 ga Yuli, 2023.
A wata hira da ta yi ‘yar jarida a shalkwatar ‘yansanda da ke Birnin Kebbi, ta ce “Wata mata ce ta nemi in taimaka mata na karbo musu sako a madadinta, daga nan na bube jakar da na ga harsashi, na isa wajen jami’an tsaron soji da ke bakin aiki a Karamar Hukumar Danko-Wasagu, sai na sauka kan mota inda na same su daga nan na yi musu bayani kuma na mika musu harsashi, in ji ta”.
A cewarta, bai dace in bari a yi amfani da wannan harsashi wajen kashe dan’Adam ba, domin a matsay-ina na Musulma ta gari me zan fada wa Allah Madaukakin Sarki ranar haduwata da shi. “Ban da wani zabi ban da in bayar da rahoto game da harsashin,” in ji ta.
“Bayan sun yi min tambayoyi su jami’an soji suka yi mani, sun kama ni, daga baya suka mika ni ga ‘yan-sanda, a cewar Hauwa Sulieman.” Sai dai ta ce, “Na san cewa mallakar harsashi laifi ne, shi ya sa na kai rahoto ga jami’an soji da ke bakin aiki a wurin da na ambata a sama,” in ji ta.
Kwamishinan, ya bayyana jin dadinsa ga mukaddashin Sufeto Janar na ‘yansanda Kayode Adeolu Egbe-tokun da ya ga ya dace da a turo shi Jihar kebbi a matsayin Kwamishinan ‘yansanda na 35.
A yayin da yake tabbatar wa IGP da gwamnatin Jihar kebbi da daukacin al’ummar jihar cewa jami’an rundunar da ke karkashinsa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ganin Jihar Kebbi da kewaye ta samu ‘yanci daga duk wani nau’i na aikata laifuka.
Bisa ga hakan ya yi kira ga jama’a a fadin jihar da su taimaka wa ‘yansanda da sauran hukumomin tsaro wajen ba da muhimman bayanai na duk wani motsi ko aiki da ake zargin laifi ne. Domin ta hanyar bayar da bayanai ne za mu iya yin aikin namu kamar yadda doka ta tana da na dakile duk wani laifi, in ji shi.