‘Yan bindiga sun hallaka wata yarinya ‘yar shekara bakwai da wasu mutum biyu a wani hari da suka kai ƙauyen Kuki da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.
Harin ya faru ne a ranar Lahadi da rana tsaka, a kusa da iyakar Kaduna da Neja.
- Sin Za Ta Yi Hadin Gwiwar Aiki Da Sauran Kasashe Masu Tasowa Domin Samar Da Ci Gaba
- Ta Leko Ta Koma, An Cire Sunan Olmo Daga Jerin Yan Wasan Laliga
Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kutsa ƙauyen ta hanyar wani gari mai suna Unguwar Mission, inda suka kashe mutum biyu da yarinyar.
Haka kuma, sun kwashe shanu da kayayyakin shaguna a yayin harin.
Wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa ya bayyana cewa an tsinci gawar yarinyar a kusa da wani daji bayan ‘yan bindigar sun gudu.
A cewarsa, ‘yan bijilanti sun bi sawun ‘yan bindigar zuwa dajin Uragi da ke Jihar Neja, inda suka ƙwato shanun da aka sace.
Shugaban Ƙungiyar Birnin Gwari, Ishaq Usman Kasai, ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai bayar da cikakken bayani ba.
Hakazalika, jami’an ‘yansandan Jihar Kaduna har yanzu ba su ce komai ba kan wannan harin.