A cikin shekaru biyar da suka gabata, ci gaban tattalin arzikin da Sin ta samu ba tare da tangarda ba, ya samar da tushe mai karfi ga ciniki, da zuba jari tsakanin Sin da Afirka, inda aka samu ci gaba mafi girma a wadannan bangarori.
Bayanan da ofishin kwastam na Sin ya fitar sun nuna cewa, tsakanin shekarun 2021 da 2024, darajar cinikin da aka yi tsakanin Sin da Afirka ta zarce dalar Amurka tiriliyan 1.1, inda aka dinga kafa sabon matsayin bajimta a wadannan shekaru 4 a jere. A cikin watanni 7 na farko na shekara ta 2025, yawan cinikin kayayyaki tsakanin Sin da Afirka ya kai dala biliyan 167, wanda ya karu da kashi 14.4 idan aka kwatanta da adadin shekarar da ta gabata, inda aka sake kafa wani sabon matsayin bajimta. A zahiri ne, harkar ciniki tsakanin Sin da Afirka tana ta samun karuwa a kowace shekara.
A cikin wadannan shekaru biyar, bangaren shigar da kayayyaki daga Afirka zuwa kasar Sin ya samu karuwa sosai. Bayanan ma’aikatar kasuwanci ta Sin sun nuna cewa, tsakanin shekarar 2021 da ta 2024, darajar kayayyakin da Sin ta shigo da su daga Afirka ta kai sama da dala biliyan 460. Kazalika, tun daga ranar 1 ga Disamban 2024, Sin ta aiwatar da matakin janye haraji gaba daya kan dukkan kayayyaki daga kasashe mafi koma bayan tattalin arziki, wadanda suka hada da kasashe 33 na Afirka da suke da alakar diflomasiyya da Sin. Har ila yau, a shekarar nan ta bana, Sin ta fadada wannan tsari zuwa kasashe 53 na Afirka. Sakamakon wadannan manufofi, shigowar kayayyaki daga Afirka zuwa Sin ta karu sosai. A cikin watanni 7 na farko na shekarar nan, darajar kayayyakin da aka shigar kasar Sin daga kasashen Afirka mafi kankantar karfin tattalin arziki ta kai dala biliyan 39.66, wadda ta karu da kashi 10.2%. Kayayyakin gona irin su Avocado daga Kenya, da kofi na Arabica daga Habasha, da koko daga Kamaru da sauran kayayyaki masu inganci na Afirka sun shiga kasuwannin Sin da yawa, suna kuma kara samar da zabi ga masu sayayya a Sin, tare da habaka masana’antu a Afirka, wanda hakan ya zama misali mai kyau na hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana a taron tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka a shekarar 2021 cewa, “A cikin shekaru 3 masu zuwa, Sin za ta karfafa gwiwar kamfanoninta, da su zuba jarin da yawansa ba zai yi kasa da Yuan biliyan 10 ba a sassan Afirka”. Bugu da kari, Sin tana ta kokari cika alkawarinta, kuma alkaluman ma’aikatar kasuwanci na kasar sun nuna cewa, a cikin shekaru 5 da suka gabata, darajar jarin da kamfanonin Sin suka zuba a Afirka ta haura dala biliyan 3 a kowace shekara. Ana amfani da wadannan kudade a bangaren samar da abubuwan more rayuwa kamar fannin bunkasa zirga-zirga, da makamashi, da masana’antu, da tattalin arziki na dijital, wadanda suka taimaka wajen habaka abubuwan more rayuwa a kasashen Afirka, tare da bude sabbin hanyoyin hadin gwiwar Sin da Afirka.
Shirin raya tattalin arziki da zamantakewar Sin karo na 14 na shekaru biyar-biyar, na tsakanin shekarar 2021 da ya 2025 yana gaf da kammalawa cikin nasara. A cikin wadannan shekaru 5, ci gaban tattalin arzikin Sin ya karfafa cinikin Sin da na Afirka matuka. Cikakken zama na 4 na kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin na 20 da ake gudanarwa a nan birnin Beijing, zai share tafarkin ci gaban tattalin arzikin Sin na shekaru 5 masu zuwa. Kana kyakkyawar makomar Sin za ta ba da damammaki masu albarka ga hadin gwiwar kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen Afirka, da bude sabon babi na hadin gwiwarsu. (Amina Xu)