A shekarar 2022 da ta gabata, baya ga tarbar tsoffi da sabbin aminan kasa da kasa da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi a birnin Beijing, ya kuma tattaki zuwa kasashen waje, inda ya gabatar da dabarun kasar Sin, domin fuskantar sauyin zamani da ba da amsa ga tambayoyin da kasashen duniya ke yi game da kasar Sin.
Ana iya cewa, harkokin diplomasiyya na shugaban kasar Sin sun bude sabon babi a harkokin wajen kasar.
Daga taron majalisar shugabannin kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai na Samarkand, da taron kolin shugabannin rukunin G20 na tsibirin Bali, da kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC, zuwa taron kolin Sin da kasashen Larabawa, da taron kolin Sin da kungiyar hadin gwiwar kasashen Larabawa dake yankin Gulf, an lura cewa, gabatar da dabarun kasar Sin domin daidaita matsalolin duniya ya kasance harkokin wajen shugaban kasar Sin na yau da kullum. A ziyarar da shugaba Xi ya kai ketare sau uku a bara, inda ya gana da shugabannin kasashe sama da 40, sun kara inganta fahimtar juna da hadin gwiwa da zumuncin dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya.
An yi imani cewa, harkokin diplomasiyya na shugaban kasar Sin a shekarar 2023, za su kai sabon matsayi, lamarin zai bude sabon babi na harkokin wajen babbar kasa mai tsarin musamman na kasar Sin. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)