Gidan Gala ko kuma gidan Dirama, wani wuri ne da ya zama matattarar samari da ‘yammata da suke halarta saboda nishadantarwa, wasu kan je domin kallon yadda samari da ‘yammata ke cashewa yayin da wani sauti ke tashi na wakokin da suke yin rawar domin birge mahalarta.
Wasu kuma sukan je domin samun budurwa da za su yi soyayya, kazalika a wasu lokutan irin wadannan gidaje sukan karbi bakuncin mayan jarumai wadanda tauraruwarsu ke haskawa a masa’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, domin nishadantarwa da kuma ganawa da masoyansu.
Alasan Ilyasu da aka fi sani da Basulo na daga cikin wadanda suka mallaki irin wannan gida na Dirama, ya yi wa wakilinmu karin haske kan abubuwan da suka shafi gidan dirama a wannan zamanin.
Ya warware zare da abawa musamman kan cewa ba ana zuwa gidan ne kawai don a yi raye-raye da nishadi ba, har aikin yi da sana’o’i ana samar wa mazauna gidan domin su dogara da kansu, kuma ya ce sun yaye yara da dama wasu duk sun koma gidajen iyayensu, wasu kuma sun yi aure.
Wannan ita ce tsaraba ta farko daga ziyarar da wakilinmu ya kai gidan diramar, muna muku albishir da cewa a mako mai zuwa za mu kawo muku kashi na biyu wanda zai kunshi wasu abubuwa da wakilinmu ya gane wa idonsa.
Amma da farko ga bayanan wadanda wakilinmu ya tattauna da su a gidan, mutum na farko Alasan Iliyasu, kana daga bisani wata ‘yar dirama da aka ci karo da ita a gidan.
Hanyoyin da suke bi domin sama wa mazauna gidan aikin yi da sana’ar dogaro da kai…
Babban abin alfarinmu a nan shi ne da muke sama wa matasa aikin yi, su wadannan yaran da kake gani daga cikinsu akwai masu ilimi mai zurfi, kuma muna binckawa domin tantance hakan, to idan muka samu irin wadannan yaran da suka zo da karatunsu, sai mu bincika mutanenmu manya da muke mutunci da su mu nemi su sama musu aiki, kuma da dama sun samu aikin yi ta wannan hanyar, ka ga wannan ai ba karamin ci gaba bane. Baya ga wannan kuma ka ga muna bunkasa al’adummu na gargajiya, kamar dai kake gani.
Yadda suke taka-tsan-tsan da yanayin rashin tsaro
A gaskiya ni dai ina da kyakkyawar fahimta da jami’an tsaro, saboda da zarar na ga wani wanda hankalina bai kwanta da shi ba na kasa a kwiwa wajen sanar da jami’an tsaro domin su tantance mana shi, sannan kuma ba ka rasa jami’an tsaro a gidan nan ko da ba’a cikin kayan aiki ba, kuma muna godiya ga ubangiji tun da muke ba mu taba samun wani tashin hankali ba.
Kalubalen karbar ‘yammata da hanyoyin da suke warware su…
Eh gaskiya mukan fuskanci hakan, amma daga baya sai muka yi wani tsari, yanzu duk yarin da ta zo nan sai mun zaunar da ita mun tambaye ta shin kina da aure, ko kuma kina da ‘ya’ya, idan duk ta ba da amsa cewa ba ta da aure, to hakan ba zai wadatar da mu ba, sai ta bamu lambar iyayenta mun tuntube sum un tabbatar da gaskiyar abin da ta fada sannan mu karbe ta. Idan kuma daga muka fuskanci karya take to ba za mu zauna da ita ba.
Hanyoyin dakile daukar ciki ga ‘yanmata…
A gaskiya ni dai tun da nake ban taba samun wannan matsalar ba, domin ni ba na irin barin yaran sakaka, irin da zarar sun ga mutum su bishi ki yi mu’amala da shi ba tare da mun san waye shi ba. Sannan ba ma yarda ma yarinya ta fita ta yi mu’amala da wani namiji kai tsaye in ma ta fita ba mu sani ba kenan, domin in son mu ne sun fi son dan abin da muke ba su ci su sha su yi hakuri da shi. Domin akwai lokaci da muke warewa mu shirya wa yarinya biki da muke kira ‘Ajo’ da za ta samu abin da za ta rufa wa kanta asiri.
Samar wa ‘yanmata kudin da za su kama sana’a ta hanyar shirya musu bikin Ajo…
Eh, gaskiya ne, akwai lokaci da muke warewa muke shirya wa yarinya biki, shi ne idan mun ga yarinya ta dan jima bata je ganin gida ba, kuma mu ga ya kamata ta je ganin gida shi ne muke shirya wannan Biki na Ajo a junanmu da abokan mutunci domin a tara mata kudin da za ta je ta gaida iyayenta.
To a nan ne za ka ga wata ta samu Naira 50,000, wata dubu 100, domin a kwanan nan akwai wacce aka yi mata ta samu kudi ya kai Naiar dubu 700, wannan ya ba ta damar bude wurin Saloon, da shagon dinki , har ta saya wa iyayenta filin da za su gina, to ka ga wannan ai ci gaba ne gare mu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp