Ɗan wasan baya na Manchester United, Harry Maguire, ya amince da ƙarin kwantiragin shekara ɗaya a ƙungiyar.
Da farko, kwantiragin Maguire, mai shekaru 31, zai ƙare ne a wannan kakar, amma sabon kocin ƙungiyar, Ruben Amorim, ya tabbatar da cewa tsohon kyaftin din zai ci gaba da taka leda a kakar nan.
Ruben ya ce Manchester United za ta yi kokarin rike Maguire har zuwa karshen kakar bana.
Ya kuma bayyana cewa Amad Diallo yana daf da kulla sabuwar yarjejeniya da kungiyar.
“Na yi magana da shi (Maguire) da safiyar yau, na kuma gaya masa cewa yana bukatar inganta wasansa a fili.
Muna matukar bukatarsa, kuma dole ne ya zama jagora,” in ji Ruben.
Maguire ya rasa mukamin kyaftin din Manchester United a karkashin tsohon koci, Erik ten Hag, amma a karkashin Ruben Amorim, wanda yake son yin wasa da ‘yan baya uku, Maguire ya sami sabuwar dama.
“Shi jagora ne, kuma muna bukatar ya kara nuna wannan jagoranci.
“Ya kamata ya inganta wasansa, domin muna fatan lashe manyan kofuna tare da shi a Old Trafford a nan gaba,” in ji Ruben.