Yau asabar 23 ga watan Satumba ne za’a fafata tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da kuma takwararta Burnley.
Wasan shine wasan sati na shida da za’a buga na gasar Premier League ta kasar Ingila.
- Brighton Ta Lallasa Manchester United Da Ci 3-1 A Old Trafford
- Bamu Da Sha’awar Daukar El Ghazi A Yanzu – Manchester United
Kungiyoyin biyu sun hadu sau 122 a tarihin wasa tsakaninsu.
A cikin wasannin Manchester United ta samu nasara har sau 60 anyi canjaras sau 21 yayinda kungiyar Burnley ta samu nasara sau 41.
Manchester United na fatan ganin ta samu nasara a wannan wasan bayan yin wasannin uku ba tare da samun nasara ba.
Yayinda ita kuma Burnley ke fatan gani ta samu nasara a wannan wasan domin samun damar barin matsayin karshen teburin Premier League.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp