Hatsarin Kwale-kwale: Rundunar Sojin Ruwan Nijeriya Ta Ceto Jami’an ‘Yansanda 8 Da Wani A Bayelsa
Jami’an rundunar sojin ruwan Nijeriya sun ceto ‘yansanda takwas da wani a wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a jihar Bayelsa.
- An Rantsar Da Sabon Shugaban Ƙasar Ghana, John Mahama
- Shugaban Ƙaramar Hukuma Ya Naɗa Hadimai 60 A Kano
Kakakin Rundunar Sojin Ruwa, Commodore A. Adams-Aliu a wata sanarwa da ya fitar, ya ce jami’an na kan hanyar zuwa Yenagoa ne, yayin da kwale-kwalen da suke ciki ya kife.
Adams-Aliu ya ce sojojin ruwan Nijeriya da aka girke a unguwar Agbura, a ranar 24 ga watan Disamba, 2024 sun yi nasarar gudanar da aikin ‘bincike da ceto’, inda suka ceto fasinjojin tara tare da bindigu 3.
Sanarwar ta ce, an bayar da agajin farko ga wadanda suka samu raunuka, daga bisani kuma aka kai su cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Yenagoa domin ci gaba da kula da lafiyarsu.