Mutane bakwai ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu biyar suka samu raunuka a wani hatsarin mota da ya afku a kauyen Gunu da ke karamar hukumar Munya a Jihar Neja a daren ranar Talata.
Kwamandan hukumar kiyaye hadura ta kasa (FRSC) a Neja, Mista Kumar Tsukwam, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai Nijeriya (NAN) a ranar Laraba a Minna cewa, hatsarin ya hada da wata mota kirar Toyota Camry da wata motar bas kirar Sharon.
- Tun Da Mu Ka Yi Sakaci Liverpool Ta Saye Gakpo, Dole Mu Sa Yi Ramos —Erig Ten Hag
- Dangantakar Sin Da Afrika Ta Kai Wani Mataki Da Babu Wanda Zai Iya Lalatawa
“Mutane 12 ne suka yi hatsarin; bakwai daga cikinsu sun mutu, yayin da wasu biyar suka samu raunuka.
“Mun samu kudi Naira 36,200, buhu daya na doya, Kyamara, caja biyu, katin gayyata aure, batirin waya daya, makullai hudu, hotuna da karamar jaka.
“An ceto wadanda suka jikkata kuma an kai su asibiti mafi kusa domin yi musu magani yayin da aka ajiye wadanda suka mutu a dakin ajiye gawa na babban asibitin Minna.
“An mika motocin ga ‘yansanda a ofishin ‘yan sanda na Munya don yin bincike,” in ji shi.
Tsukwam ya dora alhakin hatsarin a kan gudu da kuma rashin kulawa daga bangaren daya daga cikin direbobin, ya kuma shawarci masu ababen hawa da su rika kiyaye ka’idojin gudu a ko da yaushe domin gujewa hatsari.