Akalla mutum biyar ne aka ruwaito sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya auku a hanyar Ugwu Onyeama da ke Jihar Enugu.
Wannan na cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan Jihar, Dan Nwomeh ya fitar a ranar Talata.
- Gwamnatin Kano Za Ta Dauki Nauyin Karatun Dalibai 1,100
- Tattalin Arzikin Teku A Kasar Sin Ya Zarce Yuan Triliyan 9
Ya ce hatsarin ya auku ne da safiyar Talata, inda ya rutsa da fasinjoji 15, wanda hakan ya sa da dama suka jikkata.
Gwamnan jihar, Peter Mbah, ya bayyana damuwarsa kan faruwar Hatsari.
“Na yi bakin ciki da rahoton hatsarin motar da ya auku a yankin Ugwu Onyeama, kusa da Enugu wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dama tare da jikkata wasu.
“Ina mika sakon ta’aziyya ga iyalai da ‘yan uwan wadanda abin ya shafa, muna addu’ar Ubangiji ya jikan wadanda suka rasu tare da bai wa wadanda suka ji rauni lafiya.
“Gwamnati za ta binciki musabbabin afkuwar hatsarin don gujewa afkuwar irin haka a gaba.
“Ina yaba wa ‘yan Nijeriya masu kishi da kuma hukumar kiyaye hadura ta kasa kan daukin da suka kai, wanda hakan ya taimaka wajen ceto rayukan wasu da hatsarin ya rutsa da su.”