Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ta ragu zuwa kaso 23.18 cikin 100 a watan Fabrairun 2025 idan aka kwatanta da na watan Janairun 2025 mai kaso 24.48.
Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ita ce ta sanar da hakan a ranar Litinin, wata guda bayan sake kyautata ma’aunin matakin amfani na mabukata (CPI) domin samar da canje-canje a tsarin amfani.
- Wata Kotu A Abuja Ta Kori Karar Da Karuwai Suka Shigar Gabanta
- Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [13]
Hukumar ta ce an samu ragin hauhawar da kaso 1.30 idan aka kwatanta da na watan Janairun 2025.
“A matakin shekara-shekara, farashin ya yi kasa da kaso 8.52 kan wanda aka samu a watan Fabrairun 2024, wato kaso 31.70 cikin 100. Hakan na nuni da cewa an samu raguwa kan hauhawar farashin.
“Bugu da kari, a matakin wata-wata kuma, hauhawar farashin na watan Fabrairun 2025 ya tsaya kan kaso 2.04 cikin 100.”
A cewar NBS, hauhawar farashin kayayyakin abinci a watan Fabrairun 2025 ya kasance kaso 23.51 kan matakin shekara-shekara, lamarin da ke nuni da cewa an samu raguwa da kaso 14.41 idan aka kwatanta da na watan Fabrairun 2024 da aka samu kaso 37.92.
Kazalika, a wata-wata, hauhawar farashin abinci a watan Fabrairun 2025 ya tsaya da kashi 1.67 cikin dari, idan aka kwatanta da watan Janairun 2025, an samu raguwar matsakaicin farashin kayan abinci kamar su dawa, dankali, wake, masara da garin masara da rogo.
Hauhawar farashin kayayyakin masarufi a Nijeriya dai ya yi tashin gwauron zabi ne tun bayan da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya cire tallafi mai da sauyi da ya kawo kan musayar canjin kudade bayan da ya aka rantsar da shi a 2023.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp