Hauhawar farashin kayan masaruti ya kara yin tashin gwauron zabi da kashi 20, inda hakan ya haddasa tsadar kayan abinci da makamashi da kuma ci gaba da faduwar darajar Naira.
Alkaluman Hukumar Kididdiga ta Nijeriya (NBS), sun nuna cewa hauhawar farashin ya tashi zuwa kashi 20.77 a watan Satumba daga kashi 20.52 da yake a watan Agusta, wanda ba a taba ganin irin sa ba tun shekarar 2005.
- Kokarin Kasar Sin Na Zamanantar Da Kanta Za Ta Amfani Duniya Baki Daya
- Abubuwa Uku Da Zan Yi Idan Aka Zabe Ni – TinubuÂ
Kayan abinci sun yi tashin gwauron zabi zuwa kashi 23.4, idan aka kwatanta da kashi 23.1 da suke a watan Agusta.
Ana kuma ganin cewa matsin lamba zai iya sanya kwamitin tsare-tsare mai kula da kudin Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya kara yawan bashi da yake karbowa a karo na hudu a jere a watan Nuwamba.
Wannan lamarin ya sanya miliyoyin ‘yan Nijeriya shiga tsaka mai wuya, lamarin da ke sanya rayuwa kunci musamman ga masu karamin karfi.