Alkaluman hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya a watan Janairu ya tashi daga kashi 21.34 a watan Disamba zuwa kashi 21.82 cikin 100 a watan Janairu, kamar yadda Hukumar Kididdiga ta Kasa, NBS ta bayyana.
Adadin hauhawar farashin kayayyaki na Janairu 2023 ya nuna karuwar kashi 0.47 idan aka kwatanta da hauhawar farashin kayayyaki a Disambar 2022.
- Abin Da Ya Sa Zan Yi Tattaki Daga Neja Zuwa Abuja Idan Atiku Ya Ci – Aminu Hassan
- NEF Ga Buhari: Kar Ka Sake A Karkashin Mulkinka Ka Bari IPOB Ta Hana ‘Yan NIjeriya Kada Kuri’a
Ko ma dai yaya, a kowace shekara, rahoton farashin yana nan kan mataki na kashi 6.22 sama da adadin da aka rubuta a cikin Janairun 2022, wanda ya kasance kashi 15.60.
Bayanan haka kididdigar ta nuna cewa, rahoton hauhawar farashin (shekara-shekara) ya karu a cikin Janairun 2023 idan aka kwatanta da wannan watan a shekarar da ta gabata (watau Janairun 2022).
Gudunmawar abubuwa bisa ga kayyadaddun kayan da aka ambata sun hada da Gurasa da hatsi inda ya kai kashi (21.67), kazalika nau’in Dankali da Dawa ya kai kashi (7.74), yayin da kayan lambu suka kai kashi (6.06), sai kuma nau’in abin da ya shafi nama inda ya kai kaso (5.44)
A kan kowane canji da ake samu na wata-wata, an samu kari cikin watan Janairu 2023 inda ya hau da kashi 1.87, wanda ya samu maki 0.15 sama da adadin da aka yi rubuta a Disamban 2022 da kashi (1.71).
Dangane da adadi, a matsakaitan kayayyaki kuwa, matakin farashi na bai daya ya zama kashi 0.15 sama da Disambar 2022. Canjin a matsakaicin kashi na CPI na watanni 12 da ke karewa da kuma shiga Janairu 2023.