Al’ummar Arewa da ke kasuwar Umuchieze, ta yi kira ga gwamnatin jihar Abia da a tattauna domin kawo karshen matsalar tsaro da ke addabar Kasuwar Shanun da ke karamar hukumar Umunneochi.
Shugabannin al’ummar Arewa mazauna kasuwar, sun bayyana haka ne a a ranar Talata a cikin wata takarda da suka sanyawa hannu, wanda Alhaji Buba Abdullahi Kedemure ya karanta yayin wata ganawa da manema labarai a kasuwar.
- Kasuwar Shanu: ‘Yan Arewa Sun Koka Da Barazanar Korar Su A Abiya
- Yadda Mai Sayar Da Mushen Shanu Ta Fada Komar NSCDC A Gombe
Sun bayyana cewa, wasu miyagu ne ke shiga kasuwar da nufin addabar yankin ta hanyar kawo kalubalen tsaro.
Sanarwar mai dauke da sa hannun shugabanni 15 da suka hada da shugaban kungiyar, Alhaji Saleh Algare, ta ce “a bayyane yake cewa, mu ma muna fama da wadannan miyagun mutanen masu aikata laifuffuka”.
Sun jaddada cewa, lallai ana bukatar isasshen tsaro a ciki da wajen kasuwar domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a amma dai, mahukunta kasuwar sun musanta zargin cewa, kasuwar ta zama matattarar masu aikata miyagun laifuka.
Ta yi nuni da cewa, matakin da gwamnati ta dauka na korarsu daga kasuwar domin samun tsaro a yankin, zai jefa masu kasuwanci a kasuwar cikin wani hali mawuyaci da rashin tsaro.
Sun yi ikirarin cewa, tun bayan da gwamnatin jihar ta ware musu kasuwar mai fadin hekta 80 da mutane sama da 15,000 a shekarar 2005, suna zaune lafiya da jama’ar da ke zaune a yankin.