Shugabannin kungiyar ‘yan kasuwan arewa da ke kasuwar shanu ta Lobbanta Garke a karamar hukumar Umunneochi cikin Jihar Abiya sun bukaci Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu da mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ll su saka baki game da wa’adin kwanaki 14 da gwamnatin Abiya ta ba su na su fice daga kasuwar.
Mataimakin shugaban ‘yan kungiyar kasuwan shanu ta Lobbanta, Buba Abdullahi Kedemure shi ne ya jagoranci sauran shugabannin zuwa ofishin kungiyar tuntuba ta kasa (NCM) da ke Kaduna, wanda suka ce sun zo mika kokensu ne kan wa’adin korar da gwamnatin Jihar Abiya ta ba su na ficewa daga kasuwar.
- Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Nijeriya Ta Samu Ci Gaba Mai Inganci?
- An Horas Da Makiyaya Dabarun Shuka Ciyawar Shanu A Kaduna
Mataimakin shugaban kungiyar ya kara da cewa sun ‘yan kasa nagari masu bin doka wajen gudanar da harkokin kasuwancinsu a tsawon shekaru masu yawa a cikin jihar, amma a yanzu an ba su wa’adin ficewa daga kasuwan kan zargin aika-ta ta’addanci wanda suka musanta.
“Muna rokon shugabanninmu da su saka baki tare da yin kira ga gwamnan domin janye wa’adin na kwanaki 14 da aka ba mu na ficewa daga kasuwan,” in ji shi.
Shugaban kungiyar tuntuba na arewa, Dakta Auwal Abdullahi ya bayyana kudurinsa na daukan mataki a daidai lokacin da ‘yan kasuwar arewa ke fuskantar wulakanci a Abiya ko wani bangare na jihohin gabashin Nijeriya.
Ya tunatar da gwamnatin Jihar Abiya da sauran gwamnonin kudu maso gabas ce-wa ‘yan kabilar Igbo na gudanar da harkokin kasuwancinsu na biliyoyin naira a jihohin Kaduna da Kano da Katsina da ma sauran jihohin Arewa amma ba sa fus-kantar wata tsangwama.
Auwal ya ce babban aikinsu shi ne kare muradun Arewa da ‘yan Arewa bisa tsarin doka. Don haka ya yi kira ga gwamnan Jihar Abiya da ya janye wa’adin kwanaki 14 da ya bai wa ‘yan Arewa masu gudanar da sana’o’i na halal a kasuwar shanu ta Garke a jihar.
Da yake mayar da martani game da lamarin, mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan harkokin tsaro, MacDonald Ubah, wanda ya yi jawabi ga mane-ma labarai a ranar Litinin a Umuahia, ya yi watsi da jita-jita a matsayin karyar zance mara tushe.
Ya zargi masu yada wannan jita-jita da karkatar da umarnin gaskiya da gwamnati ta bayar domin haifar da rudani da bata wa Gwamna Aled Otti suna.