Mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng ya gana da tawagar ‘yan majalisar wakilan Amurka karkashin jagorancin Adam Smith a yinin yau Litinin 22 ga wata a birnin Beijing.
He Lifeng ya ce, a ranar 19 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaba Donald Trump sun yi wata tattaunawa ta wayar tarho, kuma sun cimma muhimmiyar matsaya, tare da samar da jagoranci bisa manyan tsare-tsare don tabbatar da daidaiton dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka a mataki na gaba. Kasashen Sin da Amurka na da sararin yin hadin gwiwa da kuma samun moriyar juna.
Ana sa ran Amurka za ta sa kaimi wajen yin magana da kasar Sin bisa ka’idojin mutunta juna, da zaman lafiya da samun nasara ga ko wane bangare, da kara amincewa da juna, da kawar da shakku, da sa kaimi ga habaka dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka. Ana fatan mambobin majalisar wakilan Amurka za su himmatu wajen samar da hanyoyin zantawa, da inganta tattaunawa da mu’amala, da kuma taka rawar gani wajen ci gaban kasashen biyu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp