An tsare kwamandan runduna ta ‘3 Brigade Kano’, Birgediya Janar M.A. Sadiq, a dakin tsaro na rundunar ‘yansandan Sojoji da ke Abuja, bisa zargin karkatar da tallafin shinkafa, da sayar da kayan aikin soji da suka hada da janareta da motocin aiki, ga masu sana’ar gwangwan.
Wasu majiyoyin da suka zanta da jaridar DAILY NIGERIAN bisa sharadin sakaya sunansu sun ce, hedikwatar tsaro ta kasa ta bayar da shinkafar ne ga rundunar ta kasa baki daya domin raba wa sojoji a matsayin agajin gaggawa.
- NAHCON Za Ta Biya Alhazai Diyyar Wasu Kuɗaɗe Kan Ƙarancin Kula Da Su Lokacin Hajji
- Muna Tattaunawa Don Ganin An Tsagaita Wuta A Yakin Gabas Ta Tsakiya – Kamala HarrisÂ
DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa, hedikwatar tsaro ta raba shinkafar a kalla sau uku ga sojojin Nijeriya, kamar yadda aka tsara.
Janar din da aka kulle, a cewar majiyoyi, ya raba shinkafa mai nauyin 5kg sau daya maimakon sau Uku ga sojojin sannan ya sayar da sauran.
Baya ga badakalar shinkafa, jaridar DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa, Janar din ya kwashe kayan aiki da suka hada da janaretan MIKANO a sansanin horas da sojoji da ke Falgore a Kano ya sayar da su ga dillalan ‘yan gwangwan.
DAILY NIGERIA ta tabbatar da cewa, an maye gurbin wanda ake zargin da wani tsohon magatakarda na Kwalejin Tsaro ta Nijeriya, Birgediya Janar A.M. Tukur.
Kakakin Rundunar Sojin Nijeriya, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu, bai amsa kira da sako ta wayar da aka aika zuwa ga lambar wayarsa da aka san shi ba a lokacin rubuta wannan rahoto.