An nada tsohon dan wasan Faransa Thierry Henry kocin yan kasa da shekara 21 na kasar Faransa akan kwantiragin shekaru biyu.
Tsohon dan wasan Arsenal, wanda ya taimakawa Faransa lashe gasar cin kofin duniya a gida a shekarar 1998, ya gaji Sylvain Ripoli.
Henry, mai shekaru 46, ya yi wasanni biyu a matsayin mataimakin koci a Belgium, kuma ya jagoranci Monaco da Montreal Impact.
Zai jagoranci tawagar yan kasa da shekaru 23 ta Faransa a gasar Olympics ta Paris 2024.
Henry kuma zai jagoranci yan kasa da shekara 21 wajen neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai a shekarar 2025.
Henry ya ci wa Faransa kwallaye 51 a wasanni 123, wanda kuma ya taimaka mata lashe gasar cin kofin nahiyar Turai a shekara ta 2000.