Injiniya Hassan Mohammed shi ne Sarkin Yakin Garkuwan Keffi Janar TY Buratai kuma shugaban kungiyar kwallon kafa na TY Buratai Football Academy da ke garin Keffi ta Jihar Nasarawa.
Yana daya daga cikin matasan yankin Arewacin Nijeriya masu hangen nesa a halin yanzu, wadanda Allah ya azurta da halaye irin na dattawa.
- Hukumar Harkokin Waje Ta NPC Ta Fitar Da Sanarwa Kan Kudurin Amurka Game Da Shigar Balan Balan Din Sin Samaniyar Amurka
- An Saurari Bayani Game Da Yanayin Yaki Da Cutar COVID-19 Na Kasar Sin
Injiniya Hassan ya sadaukar da rayuwarsa wajen ganin matasa sun kaurace wa duk wani abin da zai cutar da rayuwarsu sun kuma rungumi sana’o’in dogaro da kai; a kan haka ya yi ruwa ya yi tsaki wajen ganin nasarar kungiyar kwallon kafa wadda aka sadaukar da ita ga tsohon shugaban rundunar sojojin Nijeriya Janar TY Buratai, kungiyar ta zama kafar samar wa matasa abin yi wanda da dama daga cikinsu sun samu rufin asiri a harkar kwallon kafa.
Mataimakin Editanmu Bello Hamza ya tafi takanas ta Kano zuwa garin Keffi ta Jihar Nasarawa inda ya tattauna da shi, ya yi bayanai da dama a kan abin da ya shafi rayuwarsa, harkokinsa na tallafa wa al’umma da kuma yadda ya karbi karramawar da kungiyar ‘Arewarmu Duniyarmu’ ta yi masa a ranar 11 ga watan Fabrairu 2023 da mukamin Matawallen Arewa (Jakadan Zaman Lafiya) a bikin da aka yi a fadar Sarkin Bauchi da ke Jihar Bauchi, ga dai yadda hirar tasu ta kasance:
Da Farko Zamu So Mu Ji Takaittacen Tarihinka
Suna na Injiniya Hassan Mohammed an haife ni ne a shekarar 1980 a karamar hukumar Yusufari ta Jihar Yobe, na yi makarantar frimare a tsakanin garin Yusufari ta Jihar Yobe da kasar Jumhoriyyar Nijar, daga baya na dawo gida Nijeriya inda na cigaba da karatu a Federal Polytechnic Damaturu ta Jihar Yobe inda na yi ‘National Diploma’ a ‘Cibil Engineering’ sannan na kuma yi ‘Higher National Diploma’ a ‘Federal Polytechnic’ Bauchi daga baya na shiga Jami’ar Tafawa Balewa ATBU don samun babbar difloma ‘Post-graduate Diploma’ duk a bangaren ‘Cibil Engineering Technology, na kuma yi kwasa-kwasai masu yawa a bangarorin ilimi da dama.
Ta Yaya Ka Samu Kanka A Gaba Wajen Harkokin Tallafa Wa Al’umma?
Wato tun asali na taso ne a cikin iyali da al’umma da suka dauki harkokin tallafa wa al’umma da mutukkar muhimmanci, a haka na taso na ci gaba da koyi da haka, na samu karfafawar shugaba na kuma abin koyi na Tsohon Shugaban Rundunar Sojojin Nijeriya, Janar TY Buratai CFR Garkuwan Keffi, wanda ya yi matukar tasiri a rayuwa na, nima a kan haka na ci gaba da koyi da wannan hali nasa, ni kuma ina yin daidai gwargwardon abin da zan iya yi na ganin matasa sun samu kyakyawan rayuwa.
Wacce Gudummawa Kungiyar Kwallon TY Buratai Football Academy Ke Badawa Wajen Bunkasa Rayuwar Matasa?
Harkar kwallo na taka gaggaruwar rawa wajen bunkasa rayuwar matasa a sassan duniya kuma ana samun kudade masu yawa a harkar wasan kwallo a duniya, a kan haka muma a kungiyar kwallo ta TY Buratai Football Academy da aka kafa a shekarar 2021, muna fatan bayar da tamu gudumwar daidai gwargwadon yadda zamu iya. Tun da aka kafa kungiyar a shekarar mun samu nasararori da dama a wassanin da muka yi a ciki da wajen kasar nan, yan wasanmu kuma suna nuna bajintar da ya kamata a dukkan wasan da suka buga. Wannan nasarorin suna kuma samuwa ne saboda cikakkiyar goyon bayan da muke samu daga shugabanmu wato Janar TY Buratai wanna Allah ya sanya masa soyayyar ci gaban matasa, yana kuma bamu dukkan goyon bayan da muke bukata. Muna fatan wata rana zamu samu kanmu a cikin rukunin manyan kungiyoyin kwallo na kasar nan, inda zamu fitar da kasarmu kunya a matakai daban-daban.
Ya Ka Samu Kanka Da Mukamin Sarkin Yakin Garkuwan Keffi?
Kamar dai yadda ka gani, ni ina matsayin Sarkin Yakin Garkuwan Keffi ne wato, Janar T Y Buratai, shi ne aka nada a mastayin Garkuwan keffi, masarautar Keffi ta yi haka ne saboda irin gudummawarsa ga al’umma Keffi, musamman irin gaggrumar ci gaba da ya samar a masarautar Keffi da kewaye dama Jihar Nasarawa gaba daya. Bayan nada shi ne ya yi min wannan nadin na Sarkin Yakin a fadarsa, ina matukar alfahari da sarautar don duk inda aka ambaci suna na sai an hada da Sarkin Yakin Garkuwan Keffi ina kuma mutukar alfahari da hakan. A kan haka ina addu’ar Allah ya kara wa Garkuwan Keffi lafiya da tsawon kwana, Allah kuma ya albarkaci masarautar Keffi, Jihar Nasarawa da Nijeriya baki daya.
Ya Kuma Ka Karbi Sarautar Matawallen Arewa (Jakadan Zaman Lafiya) Da Kungiyar ‘Arewarmu Duniyarmu’ Ta Yi Maka?
Tabbas wannan nadin na kungiyar ‘Arerwarmu Duniyarmu’ ta zo mani a matsayin bazata, ban taba sa rai ba, sai kawai naga wasika daga kungiyar wadda shugabanta Alhaji Haruna Ibrahim da kuma sakataren kungiyar Kwamrade Isah Sulaiman suka sanya wa hannu inda suke bayanin dalilai da yadda suka cimma shawarar karramani da wannan sarauta ta Matawallen Arewa jakadan zaman lafiya wani taron su na shekara-shekara da suka yi a fadar mai martaba Sarkin Bauchi. Na yi farin cikin samun wannan yabon, musamman na fahinci cewa, dan abin da nake yi har wasu sun bi diddigi za su karrama ni a kai, hakan ya kara mani karfin gwiwa da zimmar ganin na kara kaimi wajen hidimta wa al’umma. Abin ya fi bani sha’awa a shirin taron da za a yi shi ne yadda suka tattaro mahayan dokuna daga sassan Arewacin Nijeriya inda suka baje koli tare da gabatar da wata kwarkwayar Daba wanda da mahaya fiye 150 suka halarta, ga kuma makida da mawakanmu na gargajiya suma sun baje fasahar da Allah ya basu. Addu’a na a nan shi ne Allah ya saka musu da alhairi.
Wacce Shawara Kake Da Shi Ga Matasa Musaamman A Wannan Lokacin Da Ake Fuskantar Zabe?
Yakamata matasa su fahinci cewa sune kashin bayan al’umma saboda haka bai kamata su bari wasu ‘yan siyasa da ‘yan barandan su lalata musu rayuwa ba, bangar siyasa ba alhairi ba ne, al’amari ne da ke jefa rayuwar masu yi cikin hatsari, in har bangar siyasa abin yi ne mai zai sa ‘yan siyasar ba za su kawo yaransu ba, suna can suna karatu a kasashen waje amma suna ba yaran wasu kwayoyi don su biya musu bukata. Ina mai kira a gare su da su yi karatun ta natsau, su rungumi zaman lafiya tare da sana’o’in dogaro da kai.
Menene Zaka Ce Ga ‘Yan Siyasan Kuma?
Ina kiga gare su da su ji tsoron Allah su sani cewa Allah yana kallon abin da suke yi kuma zai tambaye su ayyuykan da suka yi saboda haka su guji sanya yaran talakawa hanyar halaka. Ina amfani da wannan damar na addu’ar Allah ya zaba mana shugabanni na gari masu tausayin talakawa, Allah kuma ya sa a yi zaben lafiya ba tare da wata mastaala ba.
Me Zaka Ce Ga Wadanda Suka Samu Halartar Taron?
Ina mika godiya ta musamman ga Ambasada Tukur Yusufu Buratai CFR tsohon shugaban rundunar sojojin Nijeriya kuma Garkuwan Keffi, ina addu’ar Allah ya kare mana shi ya kuma kara masa daukaka duniya da lahira. Ina kuma godiya ga dukkan wadanda suka samu halartar taron kamar su Sadaukin Garkuwan Keffi Hon. Ibrahim Danfulani da Bulama Ibrahim Buratai, Sultan Alhassan, Col. Haruna Idris Zaria, Ibrahim Sani Garba, da kuma Injiniya Usman Ahmed Injiniya Hassan Geidam, Injjiniya Adamu Bahago Dagona, Zanna Dapchi, shugaban karamar hukumar Bursari ta Jihar Yobe, da dan majalisa wakilai, Hon. Kabir Lawal Jarman Garkuwan Keffi, Injiniya Mohammed Abbagana, Injiniya Hassan Bilal, Surb. Ali Badema, Surb. Hassan Gambo, Ali Alhaji Audu P.A, Musa Jajere, Injiniya Adamu Idi, Engr Idriss Yerima, Injiniya Adamu Ibrahim, Injiniya Mohd Ibn Adam, Mohammed Hassan Jajere, na gode kwarai da gaske.
To Ranka Ya Dade Mun gode
Nima na gode