Gwamnatin Jihar Jigawa ta kaddamar da shirin gina Rijiyar burtsatsai a yankin Lallashi na Karamar Hukumar Maigatari.
Ta yi hakan ne, domin karfafa guiwar ayyukan aikin noman rani a karamar hukumar, duba da irin yanayin da Hamada da karamar hukumar ke da shi.
- Matasa 4 Sun Yi Garkuwa Da Yaro, Sun Kashe Shi A Bauchi
- Masarautar Bauchi Ta Sauya Shawara: Za A Yi Hawan Daushe
Shirin, wanda za a yi amafani da hasken wutar sola, zai taimaka wajen yin amfani da dabarun zamani, domin noman rani.
A jawabinsa a wajen kaddamarwar, Gwamnan Jihar Umar Namadi ya bayyana cewa, shirin na daga cikin kokarin da gwamnatinsa ke kan yi, don samar da wadataccen abinci da kuma rage talauci a tsakanin talakawan jihar.
Kazalika, ya kara da cewa; gwamnatinsa ta dauki matakan da suka kamata, domin yi wa bangaren noman rani garanbawul da kuma fadada fannin, ciki har da gina dam-dam da kuma Rijiyoyin burtsatsai.
An ruwaito cewa, shirin aikin noman ranin da aka kaddamar a yankin na Lallashi, zai karade hekta 10, wanda kuma sama da kananan manoma 80, za su amfana da shirin kai tsaye.
Bugu da kari, shirin zai taimaka wajen kara samar da girbin amfanin gona mai yawan gaske tare kuma da kara bunkasa tattalin arzikin jihar baki-daya.
Malam Aliyu Musa, da yake yin jawabi a madadin sauran manoman da ke yankin ya bayyana cewa, samar da shirin a yankin da gwamnatin jihar ta yi, tamkar zuba hannun jari ne.
A cewarsa, al’ummar yankin za su ci gaba da yin addu’a, domin shirin ya dore tare kuma da ganin an kara fadada shi, don su ma sauran yankunan jihar su amfana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp