Gwamnatin tarayya ta tallafa wa manoman masara a Jihar Edo, su kimanin 25 da kayan aikin noma; ciki har da magungunan feshi.
Kazalika ta ce, hakan na daga cikin tsarinta na kokarin kara samar da wadataccen abinci a dukkanin fadin kasar.
- Manyan Jami’an Kasashen Afirka Suna Fatan Fadada Hadin Gwiwa Da Kasar Sin
- Dubban Matasan Kano Sun Yi Zanga-zangar Lumana Domin Goyon Bayan CP AI Bakori
Har ila yau, ta kuma kafa wajen bai wa manoman horo na koyon aikin noma da fasahar kimiyyar zamani.
Gwamnatin ta tallafa wa wadanda suka amfanan ne ta hanyar ma’aikatar aikin noma da samar da wadataccen abinci ta tarayya.
Manoman da suka amfana da shirin, an dabo su ne daga kananan hukumomi 18 da ke a jihar, wadanda aka horas da su kan dabarun zamani na shuka masara da yadda ake yin feshi na zamani da kuma yadda ake adana amfanin gonar da aka girbe da sauran makamantansu.
Jami’a a ma’aikatar aikin noma da samar da wadataccen abinci ta tarayya da ke jihar ta Edo, Imade Patricia a jawabinta a wajen gudanar da horon ta bayyana cewa, an tallafa musu ne daidai da tsarin gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, na kudurin wadata kasar da abinci, musamman ta hanyar yin noman masara.
Ta ce, a nan gaba; ana kuma sa ran horar da wasu dubban manoman masarar, inda ta kara da cewa; manoman 25 da suka amfana da horon, idan sun koma yankunansu za su koyar da wasu manoman horon da suka samu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp