Abdulmumin Murtala
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, wacce kuma ake kira da ‘yansandan Shari’a, a ranar Talata ta tabbatar da kama wasu mata bakwai da ta zarga da satar yadudduka da sauran kayayyaki a shahararriyar kasuwar sayar da atamfofi, Kantin Kwari a Kano.
An kama wadanda ake zargin ne tare da wani jami’in ‘yansanda da ke hada baki da su wajen aikata laifin, an kuma kama su, kamar yadda hukumar gudanarwar hukumar Hizbah ta Kano ta bayyana.
- Hutun Bikin Qingming Na Kasar Sin Ya Nuna Kuzarin Tattalin Arziki
- Duk Da Ayyana Nemansa Ruwa A Jallo, Dakta Idris Dutsen Tanshi Ya Dawo Bauchi
Da yake tsokaci kan lamarin, Shugaban Kasuwar Kantin Kwari, Hamisu Nama, ya ce wadanda ake zargin sun dade suna aikata laifi a kasuwar, musamman a lokacin cunkoso.
Ya yaba wa jami’an Hisbah bisa aikin da suka yi wanda ya kai ga cafke matan da suka amsa laifin aikata laifin yayin da yake zantawa da manema labarai.
Wadanda ake zargin sun kuma tabbatar da cewa suna zuwa kasuwar ne daga jihohin da ke makwabtaka da su domin aikata laifukan.