Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina ta lalata barasar da ta ƙwato a garin Bakori, da ke Ƙaramar Hukumar Funtua.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na hukumar, Abdul Baki Mustapha, ya fitar a ranar Lahadi.
- Sin Ta Dauki Matakan Kakkaba Takunkumi Kan Tsohon Shugaban Rukunin Tsaron Kasar Japan
- El-Rufai Ya Ƙaryata Rahoton Goyon Bayan Yanki Ko Wani Mutum A Zaɓen 2027
Sanarwar ta ce DC Bashir Lawal Balarabe tare da sauran kwamandojin Hisbah na yankin Funtua ne suka jagoranci lalata barasar da aka ƙwato.
ADVERTISEMENT
Hukumar Hisbah ta ce an ɗauki wannan mataki ne domin hana ayyukan da suka saɓa wa koyarwar addinin Musulunci tare da kare ɗabi’u da tarbiyyar al’umma.














