Mataimakin dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Sanata Kashim Shettima yace, dan uwan shugaban kasa, Hon. Fatihu Muhammad ya sauya matakin da ya dauka na fice wa daga APC.
Fatihu wanda ke wakiltar Mazabar Tarayya ta Daura da Sandamu da Mai’adua a Majalisar Wakilai, a ranar 13 ga watan Yulin 2022 ne ya bayyana ficewarsa daga Jam’iyyar APC bisa zargin da ya yi na tabka magudi da shugabancin APC ya yi a shiyyar mazabarsa.
An ruwaito dan Majalisar ya ce, ya fice daga APC ne domin abokin takararsa a lokacin zaben fidda gwani a APC ya zagi mahaifinsa wanda hakan ya fusata Fatihu nan take ya fice daga Jam’iyyar bayan abokin takararsa ya kayar da shi a lokacin zaben fidda gwanin a mazabarsa.
Sai dai, Shettima ya sanar a jiya Litinin a gidansa da ke a Abuja bayan ganawa da Fatihu, yace, dan Majalisar ya amince zai dawo cikin APC.
Shettima ya ce, Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai Rt. Hon. Ahmed Idris Wase, dan Majalisar da ke wakiltar mazabar Zango/Baure Nasiru Sani Zangon Daura, duk suma sun halarci wannan ganawar.