Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya yaba wa Gwamna Bala Mohammed bisa gina sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa da Ƙasa ta Bauchi (Bauchi International Conference Centre – ICC).
Ya ce cibiyar ta dace da yanayin duniya kuma za ta taimaka wajen bunƙasa yawon buɗe ido da zuba jari a jihar.
- Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
- Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7
Da yake magana a lokacin gudanar da taron a ranar Laraba, Obasanjo ya ce zai kasance tare da gwamnan a ko ina a duniya don jawo hankalin masu zuba jari zuwa Bauchi.
Ya ce wannan cibiyar za ta sa Bauchi ta zama cibiyar taruka, kasuwanci, da yawon buɗe ido.
Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa cibiyar alama ce ta haɗin kai da jajircewar mutanen Bauchi.
Ya kuma sanar da cewa an saka wa cibiyar sunan marigayi Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, domin girmama jajircewarsa da hangen nesansa a shugabanci.
Gwamnan ya ƙara da cewa Bauchi na da ɗimbin albarkatun ƙasa, kuma gwamnatinsa tana ɗaukar matakai don inganta yanayin kasuwanci domin jawo hankalin ‘yan kasuwa daga cikin gida da wajen ƙasa.
Taron, wanda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya wakilci shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya samu halartar gwamnonin jihohi, Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, jakadu, sarakuna, da masu zuba jari daga sassa daban-daban na duniya.
Ga hotunan: